Hukumar ICPC ta bayyana cewa a cikin shekaru huɗu ta ƙwato kuɗaɗe da kadarori na kimanin Naira biliyan 454, daga hannun manyan ɓarayin gwamnati.
Mataimakin Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Ƙididdiga na ICPC, Jude Okoye ne ya bayyana haka.
Ya yi bayanin yayin da ya ke gabatar da Kundin Nasarorin ICPC Daga 2019 zuwa Maris 2023.
Ya yi gabatarwar a ranar rufe taron kwana biyu da ICPC ta shirya wa ‘yan jarida masu ɗauko labarai a hukumar.
Dalla-dalla: Kuɗaɗen Da ICPC Ta Ƙwato Daga Hannun Ɓarayin Gwamnati:
Naira biliyan 257, waɗanda ta toshe ƙofofin da Ma’aikatu, Hukumomi, Cibiyoyin Gwamnati suka nemi karkatar da su.
Naira biliyan 3.540 waɗanda haraji ne ICPC ta ƙwato.
Manyan fulotai, maka-makan gidaje da kantina, motocin alfarma, kuɗaɗe a asusun bankuna, kuɗaɗen hayar da aka karɓa daga gidajen da gwamnati ta ƙwace, ta bayar haya, kadarori da gwala-gwalai, har na Naira Biliyan 25.36, miliyan daya 577.98, Naira biliyan 1.199, Naira miliyan 25.70, sai kuma Naira miliyan 14.83.
An yi bincike 4,737,0, kotu ta hukunta mutum 90, ta bibiyi ayyuka 3,422 a Mazaɓu duk a cikin shekaru huɗu.
Discussion about this post