Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ceto yara 9 da aka yi garkuwa da su a kauyen Goran-Namaye dake karamar hukumar Maradun.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Yazid Abubakar ya sanar da haka a wata sanarwan da ya fitar ranar Lahadi a garin Gusau.
“A ranar 3 ga Yunin 2023 rundunar ta samu labarin ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara guda tara da iyayensu suka aike su yin itace a daji a kauyen Goran-Namaye dake karamar hukumar Maradun.
“Ba tare da bata lokaci ba ‘yan sanda suka fantsama farautar ƴan bindigan sannan kuma da kokarin ceto yaran da aka sace.
“Rundunar na ci gaba da bin sawun ƴan bindigan domin kamo su da kuma hukunta su.
Rundunar ta Kuma ce a ranar Asabar din da ta gabata ‘yan bindiga sun kai hari wasu kauyukan dake karamar hukumar Maradun inda suka kashe mutane da dama a kauyukan.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin yankin Arewa dake fama da hare-haren ‘yan bindiga a Najeriya.
Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sha yi wa mutane alkawarin Samar da tsaro a kasar musamman a yankin Arewa sai dai har yanzu wannan matsala ta ki ci ta ki cinyewa.
Discussion about this post