Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASSU) da kuma Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i (SSANU), sun bayyana cewa babbar ɓaraka a Tsarin Bai Wa Ɗalibai Ramce, wanda ke cikin Dokar Manyan Makarantu da Shugaba Bola Tinubu ya sa wa hannu a makon nan.
Sai dai kuma dokar ta ce ɗaliban da za su ci gajiyar lamunin su ne waɗanda abin da iyayen su ke samu a shekara bai wuce Naira 500,000 ba, wato dala 1,000 kenan.
Wata ƙa’ida mai tsauri kuma ita ce ba za a ba kowane ɗalibin da ya cancanta ba, sai wanda ya biya kuɗin makaranta da ake kira ‘tuition fees’.
A kan haka ne ƙungiyoyin su ka ce ai shi ‘tuition fees’ tuni Jami’o’in Gwamnatin Tarayya sun daina karɓar su a hannun ɗalibai.
Saboda haka batun a dawo da biyan ƙuɗin a yanzu kuwa, abu ne da ba za su aminta da shi ba.
Ita ma Kungiyar Ɗaliban Jami’o’i ta Ƙasa (ASSU), ta yi murna da shirin lamunin, amma ba ta yarda a ƙara kuɗin makaranta ba.
Shirin Bai Wa Ɗaliban Manyan Makarantu Ramce:
Tinubu ya sa wa dokar kafa bankin bai wa ɗalibai lamuni, alƙawarin da Buhari ya yi tun 2014, har ya sauka bai cika ba.
Shugaba Bola Tinubu ya sa wa dokar kafa Bankin Ɗalibai hannu. Wannan bankin dai zai riƙa bai wa ɗalibai bashin da babu kuɗin ruwa a cikin sa.
Hadimin Tinubu Dele Alake ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa cewa Tinubu ya sanya wa dokar hannu.
Idan ba a manta ba, a cikin ‘Ƙudororin APC’, wanda Buhari ya yi kamfen da su a 2015, an rattaba cewa a farkon mulkin Buhari za a riƙa bai wa ɗalibai lamunin kuɗaɗe ba tare da an caje su kuɗin ruwa ba.
” Gwamnatin Tarayya ce za ta riƙa biya wa ɗaliban kuɗaɗen ruwan da za su biya bankin.” Haka dai Ƙudirorin da Buhari ya yi kamfen da su ya bayyana a farkon shafin daftarin.
Sai dai shi wannan ƙudiri wanda Tinubu ya sa wa hannu, tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne ya bijiro da shi tun cikin 2016.
A yanzu Gbajabiamila shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, yayin da ya fara aiki a ranar Laraba.
Wannan doka, “za ta sauƙaƙa samun damar karatu ga ‘yan Najeriya a manyan makarantun gaba da sakandare.”
Dama a kamfen ɗin Tinubu ya yi alƙawarin ganin da zarar ya zama shugaban ƙasa, to zai sanya wa ƙudirin hannu domin ya zama doka, domin inganta harkokin ilmi a Najeriya.
Discussion about this post