Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa da zai hadu da tsohon gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso a fadar shugaban kasa da ya gaura masa mari.
Ganduje ya fadi haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da yayi da shugaban Kasa Bola Tinubu.
Ganduje ya ce ya ziyarci shugaban kasa ne domin ya yi masa bayanin abinda ke faruwa a jihar Kano da orin rushe-rushen da sabuwar gwamnatin NNPP ke yi a jihar
” Na gaya wa shugaban kasa irin abinda gwamnan jihar Kano ke yi a jihar, wanda yanzu haka mutane ke yin Allah-Wadai da su.
” Ga shinan mutane sun fara tsine wa gwamnatin tun yanzu, muna da su duk mun gani. Shi kan sa gwamnan ba son haka yake yi ba, sa shi ake yi domin ɗan koro ne shi dama umarnin wani ya ke bi.
” Shi Kwankwason yana na a nan fadar shugaban kasa, da zan haɗu da shi yanzu kila da na gaura masa mari.
Ba a ga maciji tsakanin Kwankwaso da abokin sa Ganduje. Abokan juna ne a baya na kud-da-kud, amma bambamcin ra’ayi na siayasa ya raba su.
Discussion about this post