Dubban Alhazan Najeriya ne suka fake a wajen rumfunar Alhazai a Mina saboda karancin su.
Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA da ya ke wannan wuri ya ruwaito mana cewa da yawa daga cikin mahajjatan sun maƙale ne a jikin rumfunar dalilin karancin rumfunar.
Baya ga tsananin zafin rana da ake yi, ga kuma rashin wurin zama, mahajjatan Najeriya a Mina na fama da ƙarancin abincin ci.
Wani mahajjaci daga jihar Oyo da wani daga Katsina sun ce ” Gaba ɗaya yau bamu saka komai a cikin mu ba, kuma babu abincin da zamu ci ma saboda mahukunta ba su kawo ba sannan babu inda za ka siya ka ci.
Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya lura cewa rumfunar da aka ware wa dubban ƴan Najeriya ab zai ishe su ba, karshen ta dai dubbai za su rika kwana ne a waje sannan kuma ga ƙarancin abinci da suke fama da shi.
Shugaban hukumar Alhazai na kasa, Zikirullah Hassan ya bayyana cewa matsala ce aka samu daga mahukuntan kasar Saudiyya.
” Mun biya dukka kudaden da suka bukata, kuma sun bayyana mana cewa suna da makeken ɗakin dafa abinci da zai wadatar da duka Alhazan mu. Amma kuma sai muka ga ba haka ba.
Zikirullah ya ce sun tattauna da jami’an Saudiyya kuma za su ci gaba da tattaunawa domin a samu mafita cikin gaggawa.
Discussion about this post