Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Matawalle na Jihar Zamfara, Zailani Bappa, ya bayyana cewa Gwamnan na Zamfara saura kwanaki 10 su ka rage masa ya kammala wa’adin sa kan mulki. Don haka ba zai maida wa Hukumar EFCC raddi ba.
Ya ce gwamna mai barin gado ba zai maida wa EFCC zargin ya danne ko ya karkatar da Naira biliyan 70 ba.
“Saura makonni biyu kacal Gwamna ya kammala wa’adin mulkin sa. Saboda haka babu wani dalilin da zai sa ya maida wa EFCC martani ko raddi.” Inji Baffa, kamar yadda ya shaida wa PREMIUM TIMES ranar Alhamis.
Idan Matawalle ya kammala wa’adin sa nan da ranar 29 Ga Mayu, daga ranar ce rigar kariyar da dokar Najeriya ta ba shi za ta daina aiki a kan sa.
Bappa wanda ya ce shi a wurin wakilin mu ya ma fara jin zarge-zargen da EFCC ta yi wa Gwamna Matawalle, ya ci gaba da cewa EFCC na da ikon zargin kowa a kan abin da ta ke zargin an aikata ba daidai ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da EFCC ta zargi Gwamna Matawalle ya tsiyata Jihar Zamfara ƙarƙaf, ta hanyar kwashe naira biliyan 70 daga baitilmalin jihar Zamfara.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta na binciken Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, bisa zargin sa da karkatar da naira biliyan 70 daga dukiyar al’ummar Zamfara.
Kakakin Yaɗa Labaran EFCC, Osita Nwajah ne ya bayyana haka, a ranar Alhamis, lokacin da ya ke yi wa manema labarai jawabi.
Ya ce, ” maganar da ake ciki kan Gwamna Matawalle ita ce, ana binciken sa kan karkatar da naira biliyan 70 a tsari na bayar da kwangilar bogi.”
EFCC ta bayyana haka, kwana ɗaya bayan Matawalle ya nemi Shugaban EFCC Bawa ya sauka a bincike shi, saboda a cewar sa, shi ma ɗan cuwa-cuwa ne.
Nwajah ya ce “Matawalle ya karkatar da kuɗaɗen waɗanda aka karɓo matsayin lamuni daga wani banki, domin a yi wasu ayyukan raya jiha da karkara, amma sai aka karkatar da kuɗaɗen domin amfanar gwamnan. An karkatar da kuɗaɗen ga wasu makusantan Matawalle, da sunan kwangila, amma ba a yi kwangilolin ba.”
“Sama da kamfanoni 100 sun karɓi kaso daga cikin kuɗaɗen, amma babu shaidar sun yi ayyuka da kuɗaɗen.”
“Wasu da su ka karɓi kuɗaɗen, ai EFCC ta gayyato su. Sun bayyana yadda Matawalle ya tilasta su maida masa kuɗaɗen ta hannun wasu yaran sa, bayan sun canja su zuwa Dalar Amurka.”
EFCC ta ce waɗanda aka tura wa kuɗaɗen sun tabbatar mata cewa ba su yi wa Jihar Zamfara aiki ko da na gina kwalbati guda ɗaya ba.
“An riƙa maida wa Matawalle kuɗaɗen ta hannun Kwamishinan Kuɗaɗe na Zamfara da Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi.” Inji EFCC.
“Wani ɗan canji a Zamfara ya karɓi naira biliyan 6 da sunan biyan kuɗin kwangila, amma ko kwalbati bai yi ba. Ɗan canjin a Abuja ya ke.”