Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta bayyana zargin kisan kai da ‘yan sanda suka shigar a gaban kotun majistare da ke zargin Alhassan Doguwa da aikataw a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa.
Kotun dai ta zargi ‘yan sanda da tuhumar Doguwa a gaban kotun da ba ta da hurumin sauraren irin wannan laifi.
Alkalin kotun Mohammad Yunusa ya ce belin da kotun ta saka akan Doguwa na naira miliyan 500, ya haramta domin bata da hurmin sauraren irin wanna kara.
Sai dai kuma ba a nan bane maganar take domin a ranar juma’a a ka kammala bincke game da akisan rai da ake zargin Doguwa ya aikata kuma tuni a ka mika wa ofishin Antoni Janar na jihar Kano Musa Lawan wanda daga bisani za ta maka Doguwa ga kotu domin fuskantar zargin da ake masa na kisan kai.
” Za mu bi rahoton kotu dalla-dalla, bayan haka kuma zamu dauki mataki na gaba wanda zai hada da maka shi a kotu domin ya fuskanci abinda ake zarginsa da aikatawa.