Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya tabbatar wa mutanen jihar Kaduna cewa gwamnatin sa gwamnati ce da za ta yi tafiya da kowa da kowa. Ba zai nuna banbanci ba a mulkin sa.
Uba, a yayin da yake jawabi bayan rantsar da shi gwamnan Kaduna ranar Litinin ya ka kara da cewa daya daga cikin abinda zai fi maida hankali a kai shine hadin kan mutanen Kaduna da kuma ci gaba da ayyukan raya jiha kamar yadda gwamna El-Rufai ya somo.
” Ba zan yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da dawwamammen zaman lafiya a Kaduna sannan kuma da kawo ayyukan ci gaba a fadin jihar.
” Zan dauki tsauraran matakai domin bijiro da ayyukan da zasu amfani mutanen Kaduna, komai kankantansu komai kuma girman su. Babban burina shine jihar mu ta ci gaba da samun daukaka da ci gaba kamar yadda muka gada daga gwamnatin da ta wuce yanzu.
‘ Wani abu kuma da zan maida hankali sosai akai shine maganan kirkiro ‘yan sandan jihohi, A ganina hakan shine mafita tilo da ya kamata a bi domin kawo karshen rashin tsaro a garuruwan mu.
Gwamna Uba ya ce a jihar Kaduna babu bako babu dan gari, ” Mu a jihar Kaduna karkashin mulkina kowa mazaunin Kaduna dan gari ne ba bako bane, Zan rugumi kowa kuma zan yi tafiya da ko domin ci gaban mu baki daya.
Discussion about this post