Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi wa lauyoyin masu shigar da ƙara tsokacin cewa su dai ɓata lokaci su na ‘yan ƙaƙale-ƙaƙale. Ta ce su riƙa tafiya kai-tsaye a kan batutuwan da su ke jayayya a kai kaɗai.
Kotun wadda ke da manyan alƙalai biyar bisa jagorancin Babban Mai Shari’a Haruna Tsammani, ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, ranar da ta fara zaman sauraren ƙararrakin a Abuja.
Kotun dai ta fara zaman ta ranar Litinin domin fara sauraren ƙararrakin da wasu jam’iyyu da ‘yan takara su ka shigar, su na ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu a zaɓen Shugaban Ƙasa, wanda aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Sauran alƙalan da za su yi zaman alƙalancin shari’ar, sun haɗa da Stephen Adah, Misitura Bolaji-Yusuf, Boloukouromo Ugo da kuma Abbah Mohammed.
Yayin da ya ke jawabin buɗe fara zaman kotu, Tsammani ya yi wa lauyoyi tsokacin cewa kada su tsunduma cikin ƙaƙale-ƙaƙalen ba gaira ba dalili.
Ya ce yin hakan zai kawo jinkirin daɗewa ana sauraren ba’asin jawabai daga ɓangarori.
“Kun dai sani zaɓe lokaci gare shi. Kada mu tsaya mu na ɓata lokaci wajen ƙaƙale-ƙaƙalen babu buƙatar yin su. Kowane ɓangare ya bayar da haɗin kai ga ɗaya ɓangaren, ta yadda kowa daga ƙarshe zai gamsu da hukuncin da za a zartas.
“Kada ku shiga lungun ƙaƙale-ƙaƙale. Mu dai za mu duba dukkan buƙatun da su ka bijiro a gaban mu.”
Ya ce akwai ƙararraki biyar a gaban su, waɗanda za a saurara a ranar Litinin ɗin guda uku ne. Sauran biyu kuma sai ranar Talata za a saurare su.
Da ya ke jawabi, Babban Lauya Wole Olanipekun ya ce za su yi komai kamar yadda ƙa’idsr dokar ƙasa ta gindaya.
Discussion about this post