A wani bidiyon shari’ar laifin yunƙurin cira da dashen ƙoda ba bisa ƙa’ida ba da kotun Ingila ta yanke wa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu da matar sa Beatrice a ranar Juma’a, an karanto wa Beatrice dalilin da ya sa za a yi ma ta sassauci.
Mai Shari’a ya ci gaba da cewa:
1. Beatrice, kotu ta gamsu da cewa babu hannun ki wajen ƙullalliyar nemo yaron da aka yi niyyar cirar ƙodar ki don a dasa wa ‘yar ki Sonia.
2. Kuma babu hannun ki wajen ƙoƙarin da mijin ki ya yi wajen nemo wasu da aka nemi a ciri ƙoda daga ɗaya daga cikin su, bayan Asibitin Royal Family ya ƙi cire ƙodar wanda aka taho da shi nan Landan daga Najeriya.
3. Kotu ta gamsu da shaidun da aka aiko mata a kan ki cewa ke mutuniyar kirki ce.
4. Kotu ta gamsu ki na da tausayin marasa galihu.
5. Kotu ta yi nazarin irin rawar da ki ta taka ke da mijin ki wajen kafa Gidauniyar Ikewe Foundation, wadda ke taimaka wa ɗimbin marasa galihu.
6. Kotu ta yi la’akari da cewa kin shiga wannan tsomomuwa saboda tsananin tausayin halin da ‘yar ki Sonia ke ciki, har ki ka kauce hanya wajen ƙoƙarin ganin kun ceci rayuwar ta.
7. Kotu ta yi la’akari da muhimmancin uwa a wurin maras lafiya, musamman Sonia ‘yar ki. Rashin ki kusa da ita ko rashin samun kulawar ki gare ta zai ƙara sanya ta damuwa.
8. Saboda haka kotu ta ɗaure ki shekaru 4 da wata 6.
9. Za ki yi zaman kurkuku na kashi biyu bisa ukun shekarun da aka yanke maki. Bisa la’akari da cewa kin yi zaman talala a cikin gida daga 9 na dare zuwa 7 na safe, har tsawon kwanaki 240.
PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda Mai Shari’a ya karanto wa Sanata Ekweremadu na sa laifukan da kuma dalilin da ya sa shi ma ya sassauta mata tsawon ɗauri a kurkuku.
Yadda Kotun Ingila Ta Kama Ike Ekweremadu Da Laifin Yunƙurin Cire Ƙodar Mai Tura ‘Barrow’:
PREMIUM TIMES Hausa ta kalli bidiyon bayanin Mai Shari’a, inda ya riƙa lissafo irin laifukan da Ekweremadu, matar sa da likitan sa su ka yi wajen ƙoƙarin cire ƙodar wani matashi ba tare da amincewar sa ba.
Ga bayanan sa nan dalla-dalla:
Mai Shari’a: “Matashin da aka ɗauko daga Najeriya zuwa nan Ingila domin a cire ƙodar sa a dasa wa Sonia, ‘yar Ekweremadu, ya ce wa kotu ba sai ta ambaci sunan sa a yau ranar yanke hukunci ba.
Don haka a bayanin da zan yi, zan riƙa kiran sunan matashin da suna ‘C’:
1. Da da farko dai C ya tashi a ƙauyen da ko wutar lantarki da ruwan famfo babu.
2. Matsalar rayuwa ta kai shi fita daga ƙauyen su zuwa Legas tun ya na ɗan shekara 15, inda ya riƙa sayar da tarkacen kayan wayar, irin su murfin waya da ledar rufe fuskar waya (screen guard).
3. Abin da C ya ke samu a kullum bai wuce Naira 3,000 ba, kwatankwacin fam 7 na Ingila.
4. An yi masa gwajin jini a Legas, inda aka tabbatar cewa rukunin jinin sa iri ɗaya ne da na Sonia, ‘yar ka kai Ekweremadu.
5. C ya amince za ka kawo shi Ingila, amma bai san abin da ku ka ƙulla za ku yi da shi ba. Shi ya sa bai ma amince da yardar sa a cire ƙodar sa a sanya wa Sonia ba.
6. Babu wani dalilin ma da zai sa a ciri ƙodar sa a sanya wa Sonia, saboda babu alaƙa ta jini a tsakanin su.
7. Kafin a zo da C nan Ingila bai san iyalin ka ko ɗaya ba.
8. A ƙoƙarin da kai Ekweremadu ka yi na cire ƙodar C, ba ka yi wani tanadi na ɗorewar kula da lafiyar sa ba, bayan an cire masa ƙoda.
9. Akwai bambanci mai yawa da kuma tazara sosai tsakanin kai Ekweremadu da kuma C. Kai Ekweremadu babban mutum ne da ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa. Ka na da ɗimbin ma’aikata a ƙarƙashin ka. Akwai masu yi maka hidima, masu dafa wa kai da iyalan ka abinci, direbobi da sauran su.
10. Ka na da tarin dukiya da kadarorin gidaje a ƙasashe daban-daban a duniya. Gidajen ka za su kai 40.
11. Bincike ya gano a wani asusun ajiyar ka na banki ka saka fam na Ingila 450 a cikin watanni shida.
12. Shi kuwa C faƙiri ne, domin ko kuɗin motar da zai je Abuja daga Legas ba shi da su.
13. Kai Ekweremadu, matar ka da likita kun shirya haƙallar kawo C Ingila da nufin yi masa cin-moriyar-ganga, sannan ku yada kwauren ta. Alhali kuma ka na sane cewa abin da ka yi ya keta doka.
14. Kai da kan ka Ekweremadu ka na cikin sanatocin da ku ka yi dokar da ta haramta aikata irin wannan laifin da ka aikata a Najeriya.
14. Ekweremadu kai ka shige gaba wajen samar wa C bizar zuwa da shi Ingila.
15. Kai Ekweremadu, ta ɗibga ƙarya a wurin jami’an biza, ka ce C ɗan mace da ɗan namiji ya ke da Sonia. Ka ce ‘yan’uwan juna ne.
16. Kai Ekweremadu ka sake yin wata ƙaryar, wadda ka ce C ɗan’uwan ka ne na jini.
17. Kuma ka je kotu ka ji irin wannan rantsuwa ta ‘affidavit’ cewa C da Sonia ɗan mace da ‘yar namiji su ke.
18. Bincike ya nuna ka ce za a biya shi Naira miliyan 3, lamarin da kai kan ka ka san laifi ne, harƙalla ce.
19. Hujjoji sun tabbatar da cewa ka haɗa harƙalla da wata ma’aikaciyar Asibitin Riyal Family Hospital, wadda ke fassara wa C batutuwa, kuma ku ka shirya idan aka cire masa ƙoda, ita ce za ta riƙa yi masa tafintar kula da lafiyar sa, a lokacin da zai yi zaman jiyya.
20. Asibitin Royal Family ya gano akwai ƙarya a takamaimen shekarun yaron, kuma akwai mishkilar asalin ƙabilar sa, saɓanin yadda kai Ekweremadu ka nuna.
20. Waɗannan da wasu dalilai ne ya sa asibitin ya ƙi amincewa ya cire ƙodar C, ballanata har a kai ga cire ta Sonia a dasa mata ta C ɗin.
21. Ka tashi tsaye Ekweremadu. Ka na da masaniyar cewa C bai san komai dangane da ƙulle-ƙullen da ku ke yi a kan sa ba.
22. Sannan kuma ka na sane cewa C talaka ne, kuma faƙiri.
23. Ekweremadu har ƙoƙarin samun wani da za a cire ƙodar sa ka sake yi, bayan asibiti ya ƙi amincewa su cire ta C.
24. Kai Ekweremadu har mutum biyu ka yi ƙoƙarin samu domin a samu daidaiton wanda za a cire ƙodar sa, ta haramtacciyar hanyar da ku ka so yi wa C.
25. Duk da haka, kotu ta yi la’akari da kai ma ka na fama da ta ka rashin lafiyar.
25. Sannan kuma a tarihi, kotu ba ta taɓa ɗaure ka ba.
26. Tulin shaidu da aka riƙa aiko mana sun tabbatar da cewa wannan kotun ta gamsu cewa kai mutumin kirki ne.
27. Kai ke da Gidauniyar Ikewa Faundation mai taimaka wa marasa galihu. Wannan ya ƙara fito da kirkin ka a cikin al’umma.
28. Na karanta kyawawan halayen ka cikin wata wasiƙa da aiko mai shafuka 51.
29. Na yarda da kyakkyawar shaidar da tsohon Shugaban Ƙasa na Najeriya ya bayar a kan ka.
30. Kuma na yi la’akari da kyakkyawar shaida da roƙon da Majalisar Dattawa ta Najeriya da Kakakin Majalisar Tarayya na Najeriya su ka bayar a kan ka.
31. Na kuma yi nazarin wasu bayanai a kan ka, na gano kai mutum ne mai son zaman lafiya, ba a ƙasar ka kaɗai ba, har ma a wasu ƙasashe.
32. Ekweremadu masu, na saurari shaidar da ‘yar ka Sonia, maras lafiya ta bayar a kan ka.
33. Kuma na yi la’akari da cewa ka aikata abubuwan da ka aikata bisa shauƙi da ƙaunar Sonia ‘yar ka, tare da tsanannin tausayin halin da ta ke ciki.
34. Ekweremadu, na gamsu kai mutumin kirki ne, mai taimakon marasa galihu kuma wanda ya bayar da gagarimar gudummawa a dimokraɗiyya. Zan yanke maka hukunci bisa la’akari da kyakkyawan shaidun da aka yi a kan ka. Cikin masu yabon ka ɗin har da Babban Bishop na Enugu.
35. Ina ma a ce ka bi hanyar da ta dace wajen ƙoƙarin neman wa ‘yar ka Sonia magani.
Daga nan kuma Mai Shari’a ya riƙa karanto yadda kotu ta kama Beatrice matar Ekweremadu da laifi, ita da likitan Ekweremadu.
An ɗaure Ekweremadu shekaru 9 da wata 8,
sai dai Mai Shari’a ya ce zai yi kashi biyu bisa ukun adadin shekarun da aka yanke masa ne. Matar sa shekaru 4 da wata 6, sai likita shekara 10.
Discussion about this post