Kwana ɗaya kafin a ranar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, wasu tsagerun Yarabawa masu rajin ɓallewa daga Najeriya, sun kama su kafa ‘Yoruba Nation’, sun mamaye gidan radiyon Alumudun FM, a Jihar Oyo. Haka, ‘yan sanda su ka sanar.
‘Yan sanda sun ce sun kama mutanen biyar da wasu tsatsube-tsatsuben asiri da tsafi, amma ba su lahanta ko mutum ɗaya daga ma’aikatan gidan rediyo ɗin ba.
Masu rajin kafa ƙasar ‘Yorubawa Zalla dai wasu tsiraru ne daga yankin da Tinubu ya fito.
‘Yan sanda sun ce tsirarun sun shiga gidan radiyon da ƙarfin tsiya a Ibadan, da nufin su gaggauta ayyana ɓallewar su daga Najeriya.
Sun isa gidan radiyo misalin ƙarfe 6 na safiyar Lahadi, su ka ƙwace wayoyin ma’aikata, sannan su ka ayyana ɓallewa daga Najeriya, tare da kafa ‘Yuruba Nation’.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Oyo, Adebowale Williams, ya gabatar da tsirarun ‘yan a ware ɗin a gaban manema labarai.
Ya ce sun samu kiran gaggawa ne cewa wasu ‘yan a-ware sun kama gidan radiyo Amuludun 99.1 FM, da ke Moniya, Ibadan da niyyar ayyana ɓallewa daga Najeriya.
Ya ce abin da su ka aikata laifi ne, rashin kishi ne, kuma ta’addanci ne a ƙarƙashin dokar ƙasa.
Ya tabbatar cewa za su ci gaba da aikin tsare lafiya da dukiyoyin jama’a, tare da daƙile kangararrun ɓatagari.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ɗin ya shaida wa ‘yan sanda cewa wani mai suna Black Lion ne ya sa su kama gidan radiyon, su ayyana ɓalle wa daga Najeriya.
Ya ce a yanzu Black Lion ya tafi Enugu.
Discussion about this post