A ranar Alhamis ce aka ƙaddamar da littafi mai ɗauke ƙalubalen da Minista Abubakar Malami ya fuskanta a harkokin shari’ar ƙasar nan.
Littafin mai suna ‘Traversing the Thorny Terrain of Nigeria’s Justice Sector; My Travails and Triumphs,’ an ƙaddamar da shi ne makonni uku kafin saukar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan mulki.
Ofishin Ministan Shari’a a Najeriya na ɗaya daga cikin manyan ofishin ministoci masu girma da muhimmanci sosai.
A wurin ƙaddamar da littafin mai shafuka 283, Minista Abubakar Malami ya ce a tsawon shekaru takwas da ya yi ya na Ministan Shari’a, ‘yan jarida da gidajen jaridu sun riƙa ragargazar sa fiye da kima.
“An sha kiran Kakakin Yaɗa Labarai na Ministan Shari’a ana tambayar sa ya gaskiyar ji-ta-ji-tar mutuwar ta da su ka yi ana yaɗawa?”
Malami ya yi magana kan rikita-rikitar dawo da maƙudan kuɗaɗen da aka sace daga Najeriya, a zamanin mulkin marigayi Sani Abacha, sai kuma dawo da kuɗaɗen Paris Club da sauran wasu batutuwa.
Ya yi ta bugun ƙirjin cewa ofishin sa ya yi gagarimar nasarar daƙile cin hanci da rashawa.
Babban Mai Ƙaddamarwa, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, ya sayi kwafe 250 kan naira milyan 300.
Yari dai yanzu haka ya na fuskantar matsanancin binciken salwantar da biliyoyin daloli.
A wurin Malami ya ragargaji tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu.
Gwwmna Tambuwal ya sayi kwafe kan naira miliyan 125, a madadin kan sa da Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya.
Shugaban Bankin UBA, Heirs Holding da Transcorp, Tony Elumelu, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 30.
Sai kuma hamshaƙin ɗan kasuwa, Arthur Eze, Naira miliyan 10.