Rundunar ‘yan sandan dake jihar Legas ta kama wata mata mai tsohon ciki Eucharia Ndigwe mai shekara 34 bisa laifin ci zarafin ‘yar aikinta mai shekara 15.
Kakakin rundunar Benjamin Hundeyin ya ce rundunar ta kama Eucharia ranar Asabar a gidanta dake Ikeja.
Hundeyin ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna cewa Eucharia ta sa wuka ta yanka hannun ‘yar aikin ta saboda ba wanke wani jaka da ba shine aka saka ta ta wanke ba.
Ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka na rundunar za ta ci gaba da bincike akai kafin asan inda ka nufa da shari’ar.
“Yarinyar na asibitin ‘yan sanda likitoci na duba ta.
“Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a shirye take domin ta yaki duk Wani hanyar cin zarafin mata da yara kanana a jihar.
Bayan haka kwamishinan ma’aikatar kula da al’amuran mata ta jihar Anambra Ify Obinabo ta ziyarci yarinyar a asibiti domin duba lafiyar ta.
Discussion about this post