Ƙaramin Ministan Makamashi da Ƙarafa, Farfesa Abubakar Aliyu, ya ragargaji ‘yan Najeriya masu ƙorafin rashin samun wuta sosai a Najeriya.
Aliyu ya ce a Najeriya ne a duk duniya aka fi shan wutar lantarki arha takyaf, haka kuma a dai Najeriya ɗin ce a duk duniya aka fi ƙin biyan kuɗin wutar lantarki.
Aliyu ya yi wannan iƙirarin lokacin da ya ke ganawa da Kwamitin Harkokin Wutar Lantarki na Majalisar Dattawa, a zaman da aka yi da dukkan shugabannin hukumomin kula da harkokin wutar lantarki a ƙasar nan.
A zaman wanda su ka yi a ranar Alhamis a Abuja, Aliyu ya ce ya bayyana arhar kuɗin wutar lantarki a Najeriya da sauran ƙasashen Afrika, inda ya gane cewa a Najeriya aka fi shan wutar lantarki arha takyaf.
“A duk duniya a Najeriya aka fi shan wutar lantarki arha takyaf.
“Misali, ‘santi’ 15 ne a duk kilowatt ɗaya a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar kuma santi’ 42 ne duk kilowatt ɗaya.
A Jamhuriyar Benin ‘santi’ 23, Mali santi 25, Senegal santi 28, sai Burkina Faso santi 27.”
Aliyu ya yi ƙoƙarin cewa yayin da gwamnatin Najeriya ke iyakar bakin ƙoƙarin ganin ‘yan ƙasar nan sun samu wutar lantarki bakin gwargwado, su kuma ‘yan Najeriya har ma da hukumomin gwamnati ba su biyan kuɗin wutar lantarki.
Babban Manajan TCN, Sulyman Abdul’aziz, shi kuma ya nuna damuwa dangane yawan waɗanda ba su biyan kuɗin wutar lantarki a ƙasar nan.
Ya ce saboda yawan waɗanda ba su biyan kuɗin wutar lantarki ne ya sa aka ɗauke wuta kwanan nan a Kaduna da Kano.
Yayin da yake ƙoƙarin kawo shawarar da za a magance matsalolin, Shugaban Kwamitin Harken Wutar Lantarki na Majalisar Dattawa, Sanata Gabriel Suswan, ya bada shawarar cewa daga yanzu Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta riƙa cire kuɗin wuta daga kason kuɗaɗen da ta ke bai wa kowace hukumar da ta ƙi biyan kuɗin wutar lantarki.