‘Yan majalisan dake kalubalantar zaben Tajuddeen Abbas da APC ta yi a matsayin dan takarar ta na kakakin majalisar tarayya, sun mika kukan rashin amincewar su ga zaben Tajuddeen Abbas a matsayin dan takarrar kakakin majalisar tarayya ga uwar jam’iyyar APC a Abuja.
‘Yan majalisan a karkashin kungiyar Coalition of Progressive Speakers Aspirants (COPSA), sun hada da mataimakin kakakin majalisar Idris Wase, Muktar Betara, Sada Soli, Aminu Sani Jaji, Yusuf Gagdi da Miriam Unuoha.
Sun mika takardar koken na su ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.
Yadda Tinubu ya tilasta ni na janye wa Gbajabiamila a 2019
Dan majalisa Mukhtar Betara, ya nuna bacin ransa yayin da yake bayyana cewa zababben shugaban kasa Bola Tinubu da kan sa ” ya roke ni in janye daga takarar shugaban Majalisa a bar wa Femi Gbajabiamila yayi.”
Ya kara da cewa ya janye daga takarar shugaban kasa a 2019 bisa rokon da Tinubu, wanda a lokacin jigo ne a jam’iyyar.
” Za mu gwabza da Femi Gbajabiamila ne a 2019, Tinubu ya kira ne ya ce ina so ka bar Femi ya ya zama kakakin majalisa, domin zai yi murabus daga aikin majalisa daga wannan zangon.
” Dukkan mu a lokacin muka hada karfi da karfe muka tabbatar Gbajabiamila ya yi nasara. Shi da kan sa Tinubu ya sake kira na ya ce Betara, ina rokon ku ku taya Femi rike wannan majalisar, na ce mishi toh baba.
Bayan haka Betara ya yi suka ga yadda aka kai mataimakin shugaban majalisar dattawa yankin Arewa Maso Yamma da kuma kakakin Majalisar Dattawa Arewa maso yamma, duk yanki guda, ya ce ba a taba yin haka.
” Ba a taba raba mukamin manyan shugabannin majalisa biyu zuwa yanki daya ba, wannan babu adalci a cikin sa ko kadan.
Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya roki yan majalisan su maida wukaken nasu su kwantar da hankula, cewa jam’iyyar za ta duba wannan kuka na su kuma lallai za a yi tafiyar nan tare ne.
An ci Amanar mu – Wase
Mataimakin kakakin majalisar Tarayya, Idris Wase ya ce a ganin su jam’iyyar APC ta ci amanar su ne zabar Tajudden Abbas da aka yi wai shine zabin jam’iyyar.
” Mun bada gudunmawar matuka domin nasarar jam’iyyar APC da ita kanta majalisar. Kuma muna sa ran za abamu damar mu fito domin zama shugaban majalisar wakilai ammam abinda aka yi a gaskiya kamar cin amana ce aka yi mana.