Wata matan aure mai suna Oluwatoyin Falade ta roki kotu da ta raba auren ta da mijinta Segun bisa zargin bibiyan mata da rashin kula.
A zaman da kotun ta yi ranar Laraba Oluwatoyin ta bayyana a kotun cewa saboda tsananin bibiyan mata da mijin ta yake yi har tsakalar ta ake yi a unguwar su.
“Na auri Segun shekaru 11 da suka wuce kuma mun haihu ‘ya’ya biyu mata masu shekaru 11 da 8.
“Ina Kuma da wasu mata biyu da na haifa a aurena na farko suna da shekaru 18 da 15 amma ban iya zama da su ba saboda tsoron kada mijina na yanzu ya far musu suma.
“Segun baya kula da ni da ‘ya’yan mu. ni ne dai nake kula da gida.
Segun ya amsa laifin da ake zargin sa dashi amma kuma ya roki kotu ta bashi dama domin yana kokarin daina wannan hali.
“Tun tuni nake rokon Oluwatoyin da ta yi hakuri kada ya kaiga sai mun zo kotu ammam taki. Lallai ina kokarin daina wannan hali nawa na bin mata.
“Amma Ina kokari na wajen kula da iyali na domin ko a ido za a ga babu wahala a jikin Oluwatoyin da ‘ya’yana.
Alkalin kotun Adewale Adegoke bayan ya saurari ma’auratan ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 30 ga Mayu.
Discussion about this post