Hukumar EFCC ta ƙaryata zargin da Gwamna mai barin gado na Zamfara, Bello Matawalle ya yi wa Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, cewa zargin ya nemi ya ba shi toshiyar baki ta dala miliyan 2, ƙarya ce.
Matawalle ya yi wannan zargin a cikin wata hira da ya yi da Gidan Radiyon BBC Hausa.
Matawalle dai na fama da shan bincike a ƙarƙashin EFCC, wadda ta ke zargin ta da yin rub-da-ciki da naira biliyan 70 na al’ummar Jihar Zamfara.
Matawalle ya zargin EFCC da damuwa kan gwamnoni kaɗai, maimakon su matsa lamba har a kan Ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati.
A cikin hirar da BBC ta yi da shi, ya sake ƙalubalantar Bawa cewa a sauka a yi binciken shi kan sa.
“Ina tabbatar da cewa idan ya sauka cikin sakan kaɗan sai an samu takardun ƙorafi a kan sa kamar 200.”
Matawalle ya ce shi kan sa Bawa ya nemi ya ba shi dala miliyan 200, har ya tura masa wani ɗan-koren sa.
Ya ce saboda bai samu ba, shi ya sa ya ke ta bin sa da bi-ta-ƙulli.
“Ya nemi na ba shi cin hancin dala miliyan 2. Kuma ina da shaida. Kuma shi ma ya san gidan da mu ka haɗu ni da shi. Ya ce min gwamnoni su na zuwa su na ganin sa a ofis, amma ni ba ni zuwa.
“Idan ba ni da hujja, ai ba zan riƙa furta irin waɗannan maganganu ba.” Inji Matawalle.
Sai dai kuma Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya ce ƙarya Matawalle ke yi. Kuma idan ya na da shaidu ko hujja, to ya fallasa.
Discussion about this post