Ministocin Shugaba mai barin gado, Muhammadu Buhari su biyu, sun bayyana cewa ƙirƙiro Ofishin Ƙaramin Minista bai halasta ba a bisa dokar tsarin mulkin Najeriya.
Tsohon Ƙaramin Ministan Ƙwadado Festus Keyamo da Ramatu Aliyu, Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya, Abuja, sun ce muƙaman da su ka riƙe tsawon shekaru huɗu haramtattu ne, sun saɓa doka.
“Ya Shugaban Ƙasa, shi muƙamin Ƙaramin Minista dagula tsarin doka ne kawai, saboda ba shi da wani amfani a wasu muƙaman da dama.” Haka Keyamo ya bayyana a lokacin da ya ke jawabin bankwana a zaman Majalisar Zartaswa na ƙarshe, wanda bayan zaman ne Shugaba Buhari ya rushe ministocin baki ɗayan su, a ranar Laraba.
Gwamnatoci da su ka gabata tun kafin Buhari sun riƙa ƙirƙoro muƙaman Ƙaramin Minista don kawai a saka wa ‘yan siyasar da su ka yi wa jam’iyya hidima a lokacin kamfen.
Hakan ya sa wasu da ake kira Ƙaramin Minista, da yawan su sai su shekara huɗu har su kammala da yawan mutane ba su san da su ba, kuma babu wani takamaiman aikin da suke yi mai muhimmanci.
Keyamo ya ce Sashe na 147 na Kundin Dokokin Najeriya, wanda sashen ne ya ƙirƙiro Ofishin Minista, bai ƙirƙiri Ofishin Ƙaramin Minista ba.
Haka ya ce ba daidai ba ne Majalisar Dattawa ta tantance mutum a matsayin “Minista”, amma daga baya a zo a naɗa shi Ƙaramin Minista.
Keyamo wanda aka daina jin ɗuriyar sa a matsayin Ƙaramin Minista, ya koma ya na Kakakin Kamfen ɗin Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu, tun da farko dai an naɗa shi matsayin Ƙaramin Ministan Neja Delta, amma daga bisani aka maida shi Ƙaramin Ministan Ƙwadago.
A jawabin bankwana da ya ke yi wa Buhari, ya ci gaba da cewa shugaban ƙasa ba shi da hurumin maida mutum wai Ƙaramin Minista, bayan Majalisar Dattawa ta tantance shi a matsayin Minista.
Sai dai kuma ya yi nuni da cewa ba wai rashin-godiyar-Allah ya ke yi wa Buhari ba, ya na bayyana abin da doka ta tanadar ne kawai.
Ita ma Ramatu Aliyu ta nuna rashin jin daɗin yadda ba a ɗaukar Ƙaramin Minista da muhimmanci, alhali kuma ana ɗauko kowane daga jihar sa a matsayin Minista kamar kowa, har a wurin tantancewa a Majalisar Dattawa.
Discussion about this post