Manyan sanatoci uku da ke sahun gaba wajen tseren hawa kujerar Shugaban Majalisar Dattawa duk sun sha fama da kiciniyar yadda za su ƙwaci kan su daga hannun Hukumar EFCC, biyo bayan damƙar da aka riƙa yi masu mai nasaba da salwantar biliyoyin kuɗaɗe a hannun su, tsawon shekaru 16.
Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio na a sahun gaban neman shugabancin Majalisar Dattawa. Ya na ɗauke da lodin zargin karkatar da biliyoyin kuɗaɗe, tun lokacin ya na gwamna da kuma lokacin da ya ke Ministan Harkokin Neja Delta.
EFCC ta taka cikin sa ta nemi naira biliyan 108 bayan ya sauka gwamna cikin 2015, amma amayar da kuɗaɗen ya faskara.
Kwanan nan kuma EFCC ta buga masa kiranyen ya kai kan sa hedikwatar hukumar da ke Abuja, domin a tatsi wasu kuɗaɗen da ba a faɗi adadin su ba, kuma ba a ambaci a wurin da aka kwashe kuɗaɗen ba.
Duk da wannan baranƙyanƙyama, hakan bai hana jam’iyyar APC, Gwamnonin Arewa da shi ma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu ƙoƙarin ɗaure masa gindi domin su ga ya zama shugaban majalisar dattawa.
Idon APC ya rufe, sun kauda kai daga dukkan zarge-zargen da ake yi wa Akpabio, su na ta ƙoƙarin su ga ya zama shugaban majalisar dattawa.
Akpabio, Orji Kalu da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari duk su na sahun tseren ganin sun zama shugaban majalisar dattawa.
Sauran da su ka rage irin su Barau Jibrin, Sani Musa da Osita Izunaso, ba a bibiyi tarihin siyasar su an same su tabon rashawa da cin hanci a jikin su ba.
Orji Kalu dai har ɗaure shi an yi hukuncin shekaru 12. Ya yi zaman kurkuku tsawon watanni shida, sai Ƙotun Ƙoli ta sake shi, ta ce sai an sake shari’ar. Har yau ba a sake shari’ar ba.
Gararumar Abdul’aziz Yari Ta Biliyoyin Nairori, Wadda PREMIUM TIMES Hausa Ta Buga, Cikin Afrilu, 2022:
Tsohon gwamnan da ya taya akanta jidar naira biliyan 84, ya yi wa malamai da ‘yan APC watandar shanu 370, ragunan layya 3,500 a Zamfara.
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya yi watandar shanu 370 da raguna 3,500 ga shugabannin APC na mazaɓu da ƙananan hukumomi, malamai da kuma marasa galihu.
Yari, wanda a yanzu haka EFCC ke tuhumar sa da taya tsohon Akanta Janar kantara satar naira biliyan 84, ya kuma yi bindiga da naira, miliyan 290 a lokacin Umrah a Saudi Arabiya.
Shugaban Kwamitin Rabon Shanu da Ragunan Layya na Yari, wato Shugaban APC na Jihar Zamfara, Lawan Liman, ya shaida cewa Yari ya yi watandar ce domin taimakawa a samu naman Sallah da kuma yin layya.
An dai yi raba shanun 370 ga jiga-jigan APC tsoffin ‘yan alewar da su ka daɗe a cikin jam’iyya, da kuma sabbin-yanka-raken da suka bar PDP su ka koma APC.
Dama kuma cikin makon ne aka raba ragunan layya har 3,593, da nufin taimaka wa marasa ƙarfin aljihu su yi layya.
Waɗanda su ka amfana har da malamai, matasan APC, Reshen Matan APC da sauran marasa galihu a faɗin jihar Zamfara.
PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda Abdul’aziz Yari ya taya Akanta Janar Jidar naira biliyan 84.
PREMIUM TIMES ta damƙe wasu sahihan bayanai masu ɗauke da dalla-dallar yadda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya haɗa baki da Akanta Janar (AGF) su ka jidi naira biliyan 84, wadda EFCC ke ƙoƙarin ƙwaƙulowa daga hannun su a yanzu.
Masu bincike sun tabbatar da cewa, daga cikin naira biliyan 20 da Yari ya jida, ya yi bindiga da dala $700,000 cikin kwanaki kaɗan, a tafiyar sa Umra cikin azumi.
EFCC na binciken Ahmed Idris da Yari su ka jidi naira biliyan 84 cikin watanni 10, wato daga Fabrairu zuwa Nuwamba, 2021.
Yayin da an bayar da belin Ahmed Idris, shi kuma Yari har yanzu ya na tsare ana yi masa tambayoyi da bincike.
Masu masaniyar binciken sun ce kuɗaɗen da Ahmed da Yari su ka sata, sun kamface su ne daga kuɗaɗen kashi 13% bisa 100% na kason da ake ba jihohi takwas masu arziki man fetur.
An tabbatar da cewa Akanta Janar ya karkatar da naira biliyan 84 ta hannun wani kamfanin tuntuɓa na wani mai suna Gbenga Akindele. Sunan kamfanin Westgate Projects Limited.
EFCC ta ce ba wani aiki kamfanin Westgate Projects Limited ya yi ba, sai dai kawai an yi amfani da shi ne “an yi gadangarƙamar sata.”
Idris da Yari sun haɗa baki da wasu jami’an Hukumar Rarraba Wa Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi Kuɗaɗe (RMAFC) da kuma wasu jami’an jihohin tara wajen handame kuɗaɗen da sunan gudanar da ayyukan tuntuɓa.
Majiya ta ce bayan an tura wa Akindele naira biliyan 84, sai shi kuma ya fara rabawa tsakanin waɗanda aka shirya gadangarƙamar satar da su.
PREMIUM TIMES ta kasa jin ta bakin Akindele, sannan kuma kamfanin na sa ko sunan sa ma babu a shafin yanar gizo.
‘Mugu Shi Ya San Makwantar Mugu:
Majiya ta ce Yari ya danne kashi ɗaya na kuɗaɗen, sai ya bai wa Akanta Janar Naira biliyan 22.
Yari ya tashi da Naira biliyan 20, yayin da jami’an Hukumar RFAMC Naira biliyan 16. Wasu maƙudan kuɗaɗen da ba a san ko nawa ba ne kuma, sai aka miƙa su ga jami’an jihohin da ya kamata a tura wa kuɗaɗen.
Masu bincike sun ce Yari ya karɓi na sa kason ta hannun wani mai suna Anthony Yaro, na wani kamfani mai suna Finex Professionals Services.
EFCC sun tabbatar cewa Yaro ɗan-koren Yari ne.
Yadda Abdul’aziz Yari Ya Yi Bindiga Da Naira Miliyan 290 Lokacin Umrah A Saudiyya -EFCC
Jami’an EFCC sun ce dala 700,000 ɗin da Yari ya kashe a Saudiyya, ta na daidai da Naira miliyan 290.
Kuma ya kashe su ne wajen biyan kuɗaɗen kwana otal, zirga-zirgar hawa jirage da sauran saye-sayen tsaraba na ba gaira babu dalili.
EFCC ta ce Yari ya tafi Umrah tare da ɗimbin hadimai, ‘yan’uwa da makusanta.
Kakakin Yari, Mayowa Oluwabiyi, ya ce ba zai yi magana ba, tunda batun ya na hannun EFCC.
A farkon makon nan Premium Times Hausa ta buga labarin yadda EFCC ta kama tsohon Gwamnan Zamfara, ta na neman ƙwaƙulo naira biliyan 20 a hannun sa.
Zaratan EFCC sun cumuimuyi tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari, ta yi awon gaba da shi, bayan an gano ya na da hannu wajen tara Akanta Janar Ahmed Idris kantara satar naira biliyan 80.
EFCC ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ta kama Yari a gidan sa da ke Abuja, bayan bincike ya nuna cewa ya jidi naira kusan biliyan 20 daga cikin naira biliyan 80 ɗin da EFCC ke nema wajen Akanta Janar.
EFCC dai ta kama Ahmed Idris ne cikin makon shekaranjiya, bisa zargin karkatar da naira biliyan 80 da aka ba shi amanar ajiyewa cikin kuɗaɗen Najeriya.
An damƙi Yari a ranar Lahadi a Abuja, kwanaki kaɗan bayan ya ci zaɓen fidda-gwanin Sanatan APC na Zamfara ta Yamma ba hamayya.
An dai yi cacikui da Ahmed Idris tun a ranar 16 Ga Mayu.
A cikin 2021 EFCC ta sha kama Yari bisa binciken yadda ya karkatar da biliyoyin kuɗaɗe, wato wasu daban ba waɗannan biliyan 20 da ake magana a yanzu ba.
Ya yi Gwamnan Jihar Zamfara daga 2007 zuwa 2019.
Kiranye Daga Bawa: EFCC Ta Ce Akpabio Ya Kai Kan Sa A Tatsi Biliyoyin Nairori A Ruwan Cikin Sa:
Makonni biyu da su ka gabata, Hukumar EFCC ta nemi Sanata Godswill Akpabio, kuma tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, cewa ya bayyana domin ta bincike salwantar maƙudan kuɗaɗe a cikin aljifan sa.
Akpabio, wanda sanata ne daga jihar Akwa Ibom, ya na a sahun gaban waɗanda yanzu haka ke takarar neman zama Shugaban Majalisar Dattawa.
EFCC ta ce Akpabio ya kai kan sa hedikwatar hukumar a ranar 9 Ga Mayu.
Sanarwar ta biyo bayan wata wasiƙa da aka aika wa lauyan sa Umeh Kalu tun a ranar 13 Ga Afrilu.
Akpabio, wanda tsohon gwamnan Akwa Ibom ne, an gayyace shi a cikin watan Maris, amma sai lauyan sa Kalu ya rubuta wa EFCC wasiƙa a ranar 27 Ga Maris, ya ce Akpabio ba zai samu kai kan sa ofishin EFCC ba, saboda a ranar ya na da ganin likitan sa a ƙasar waje.
A cikin wasiƙar dai lauyan ya ƙara yi wa EFCC bayanin cewa Akpabio na fama da ciwon limoniya, kuma zuciyar sa kan fuskanci tsaikon bugawa.
Akpabio, inji lauyan sa ya na fama da matsalar yin numfashi yadda ya kamata, kuma ya na jin ciwo idan ya na numfashi, shaƙar iska na yi masa wahala.
A kan haka ne lauyan ya ce Akpabio zai iya kai kan sa ofishin EFCC bayan azumin Ramadan.
Sai dai ba a san dalilin gayyatar Akpabio shin wasu kuɗi ne ake tuhumar yasa salwantar a Ma’aikatar Harkokin Neja Delta, ko kuwa tun waɗanda EFCC ta fara tuhumar sa ne kimanin naira biliyan 108 a 2015, bayan ya kammala gwamna.
Kurarin Orji Kalu Bayan Ya Fito Daga Kurkuku: Ƙarfin arziki na ya fi ƙarfin na ɓuge satar naira biliyan 7.65:
Cikin watan Janairu, 2922 PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da Kalu ya ce bai saci kuɗaɗen da aka ɗaure shivm a kan su ba.
A labarin, tsohon Gwamnan Jihar Abia, Sanata Uzor Kalu, ya bayyana yadda ya fara sana’a da yadda ya zama biloniya tun ma kafin a kafa PDP.
A tattaunawar da ya yi da gidan talbijin na ARISE TV mallakar Thisday a ranar Alhamis, Kalu ya ce ya fara kasuwanci da sana’ar sayar da man ja, tun ya na ɗalibin jami’a a Maiduguri.
“Lokacin da ina Jami’ar Maiduguri, sai na fahimci sana’ar man ja na da tasiri a garin sosai. Saboda ana buƙatar sa, amma babu manyan dilolin sa.
“To idan na tafi gida hutu, sai na lodo man ja mai yawa na kawo Maiduguri na sayar ga manyan ‘yan kasuwar man ja.”
Kalu wanda shi ne Bulalar Majalisar Dattawa, ya ce daga nan ya yi sana’ar sayar da kifi. Da ya zama attajiri ne kuma ya koma hada-hadar ɗanyen mai, sugar, kuma ya zama babban dilan sayar wa Sojojin Najeriya makamai. Kalu ya riƙa kai wa sojoji kayan abinci a bakin daga.
A cikin tattaunawar, ya bada labarin cewa ya haɗu da tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Babangida da Buhari tun zamanin mulkin soja, sannan su na manyan hafsoshi. Amma bai bayyana irin yadda su ka taimaka wa rayuwar sa ba.
Kalu shi ne mai jaridun The SUN da Telegraph.
Da Ruben Abati ya yi masa tambaya kan ɗaure shi da aka taɓa yi akan shari’ar zargin satar naira biliyan 7.65, Kalu ya ce wannan duk sharri ne magauta su ka ƙulla masa domin ganin bayan sa.
“Kai Ruben ka san ni sarai tun ma cikin 1992. Tun kafin na zama gwamna ni ƙasaitaccen attajiri ne wanda ya fi ƙarfi ya saci naira biliyan 7.65, har sunan sa ya ɓaci a ce masa ɓarawo.
“Da mulkin siyasa ya dawo, ni na bai wa PDP zunzurutun kuɗi Naira miliyan 500 a farkon kafa ta. Da Obasanjo ya fito daga kurkuku kuma ni na fara ba shi kuɗi masu yawa. Naira miliyan 100 na ɗauka na ba shi.” Haka Kalu ya taɓa faɗa a wata hira da jaridar Guardian ta taɓa yi da shi cikin 2019.
Kalu ya ce bai yiwuwa a ce shi da ya fara kashe wa PDP kuɗi tun farkon kafa ta zamanin mulkin soja, sannan don ya zama gwamna ya ɓuge da satar naira biliyan 7.65.
Ya ce masu jin haushin ya zama ƙasaitaccen attajiri ne tun ya na matashin sa.
A cikin hirar, ya bada labarin cewa har haɗa ƙwanjin takarar shigo da sugar ya yi shi da Ɗangote.
Ranar Talata ce wannan jarida ta buga labarin Kalu na cewa zai fito takarar shugaban ƙasa, idan APC ta damƙa wa Kudu maso Gabas takara.
Yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke ƙaratowa cikin 2023, Bulalar Majalisar Dattawa, Orji Kalu ya bayyana cewa zai fito takarar shugabancin Najeriya, idan har jam’iyyar APC ta damƙa takarar ga yankin Kudu maso Gabas, wato yankin ƙabilar Igbo.
Haka tsohon Gwamnan na Jihar Abia ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai (NAN), yayin komawar sa Abuja, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, a ranar Talata.
NAN ta ruwaito Kalu na cewa ƙungiyoyi da dama sun nemi Kalu ya fito takarar shugabancin ƙasa, kuma sun bayyana cewa a shirye su ke domin su tabbatar cewa ya yi nasara a zaɓen 2023.
Sannan kuma an ga fastocin Kalu na neman takara an manna a kan titinan jihohin ƙasar nan da dama.
Yayin da ya ke yaba wa ƙungiyoyin da ke neman ya fito takara, mawallafin jaridun The Sun ya ce gani su ka yi shi ne ya fi cancanta, shi ya sa kowa ke rububin sa.
Ya ce tabbas shi ma ya ga fastocin sa sun cika garuruwa shi ya ƙara masa ƙwarin guiwar neman fitowa takara.
Sai dai ya ce shi zai yi biyayya ga jam’iyyar APC mai mulki. Saboda takarar sa na da sharaɗin cewa sai idan APC ta damƙa wa Kudu maso Gabas takara, sannan zai fito gadan-gadan.
“Ina mai godiya ga jama’a masu mammanna fastoci na a garuruwan Najeriya. Ni ban ce zan tsaya takara ko ba zan tsaya ba. Amma dai idan aka damƙa takara ga Yankin Kudu maso Arewa, to tabbas zan fito gadan-gadan.
“Amma dai na san cewa jam’iyyar mu za ta tsayar da ɗan takarar da zai haɗa kan Najeriya. Kuma dama hakan shi ne mafi muhimmanci ga ɗorewar ƙasar nan.” Inji Kalu.
Discussion about this post