Hatsabibin ɗan ta’adda Dogo Giɗe, ya sako sauran ɗalibai mata biyu na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da su ka rage a hannun sa, bayan an cika masa Naira miliyan 45 da ya nema.
An sako sauran ɗaliban biyu mata a ranar Laraba da dare, bayan sun shafe kwanaki 707 a hannun sa.
Matan biyu su ne Farida Kaoje da Safiya Idris.
Mahaifin Farida mai suna Sani Kaoje, ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa kafin a saki yaran biyu sai da su ka biya Naira miliyan 45 ga la’anannen ɗan ta’adda, Dogo Giɗe.
“Da farko kafin ya fara sakin wasu daga cikin yara 11 ɗin da su ka rage a hannun sa, sai da muka sayar da dukkan kadarorin mu, mu ka nemi taimako, har mu ka haɗa masa Naira miliyan 80. Amma sai ya ƙi sakin su gaba ɗaya.
“Ya ƙi sakin ɗaliban duka, saboda wasu daga cikin takardun kuɗaɗen da mu ka kai masa sun lalace. Sai ya maido mana su. Mu kuma mu ka kai wa gwamnatin lalatattun kuɗaɗen da ya maido mana ɗin.
“Daga nan kuma sai ya sake neman Naira miliyan 45. Amma tunda ba mu da saukan komai, sai mu ka tunkari gwamnati, kuma mu ka nemi taimako a hannun masu hali, har mu ka haɗa masa abin da ya nema.” Inji Kaoje, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya yi ritaya.
Kaoje ya ƙara da cewa a ranar Laraba sai Dogo Giɗe ya kira wani Abubakar wanda shi ne mai shiga tsakani, tare da iyayen yaran su biyu.
Ya ƙara da cewa an wuce da matan biyu asibitin Birnin Kebbi, domin a duba lafiyar su.
Cikin 2021 ne Dogo Giɗe ya yi garkuwa da sama da ɗaliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri su 100.