Kotun Ƙoli ta kori ƙarar da PDP ta shigar, wadda tun da farko ta nemi a soke takarar da Bola Tinubu ya shiga, ta neman shugabancin Najeriya, bisa zarge-zargen cewa bai cancanta ba.
Haka kuma a cikin ƙarar PDP ta ce Mataimakin Takarar Tinubu, wato Kashim Shettima, bai cancanta ba shi ma.
Lokacin da PDP da shigar da wannan ƙara dai ta nemi kada a rantsar da su a ranar 29 Ga Mayu, 2023.
Alƙalai biyar ne suka yanke hukuncin, bisa jagorancin Inyang Okoro, kuma sun kori ƙarar a ranar Juma’a.
Babban Mai Shari’a Adamu Jauro ne ya karanta hukuncin kotun, a madadin sauran alƙalan huɗu da shi kan sa cikon na biyar.
Sun yanke hukuncin cewa PDP ba ta da damar shigar da ƙara a cikin lamarin harka ta cikin gidan APC.
“Ya na da kyau masu shigar da ƙara su sani cewa babu ruwan wata jam’iyya da lamarin tsayar da ɗan takarar zaɓen wata jam’iyya.
“Babu jam’iyyar da ke da haƙƙin ƙalubalantar INEC dangane da sha’anin zaɓen fidda-gwanin wata jam’iyya ko jayayya kan ɗan takarar da wata jam’iyya ta tsaida.
“Haka nan kuma babu wata kotu da ke da ikon sauraren ƙarar zaɓen fidda-gwanin ɗan takarar da wata jam’iyyar daban ta tsayar da shi.”
Kotun Ƙoli ta ce PDP ta kasa gabatar da hujjojin da ke nuna aibu ko cikas ɗin da ta samu, kasancewa Kashin Shettima ya yi rajistar shiga zaɓe wuri biyu, wato zaɓen mataimakin shugaban ƙasa da kuma takarar sanata a Jihar Barno.
Discussion about this post