Tabbatattun bayanai na nuna cewa ɗaruruwan ‘yan bindiga a ƙarƙashin tsigirin fitinannen ɗan ta’addan nan mai laƙabin Ɗanƙarami sun yi hijira daga Zamfara, sun kwarara cikin ƙananan hukumomin Safana da Batsari a Jihar Katsina.
Mazauna ƙauyukan waɗanda su ka riƙa ganin tuɗaɗowar maharan sun ce sun yi hijira ne daga Zamfara saboda fatattakar su da sojoji ke yi a yanzu.
An tabbatar da cewa an ga irin su a yankunan Tsaskiya, Runka, Gora, Labo da wasu ƙauyuka na cikin ƙananan Hukumomin biyu.
Mazauna yankin sun ce gudaddun ‘yan bindiga ɗin sun haɗe da gungun dabar ɗan ta’adda Usman Moɗi-Moɗi, wanda a yanzu ke sharafin kai wa mutane farmaki.
Waɗanda su ka gan su sun ce ‘yan ta’addar sun shigo Jihar Katsina da manyan makamai sannan kuma garke-garke na shanu masu ɗimbin yawa.
“Kusan su dubu ɗaya su ka kwararo a kan babura kusan 300. Sun yada sansani a ƙauyen Labo a ranar Asabar, kuma a can su ka kwana.” Haka dai wani ganau ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya.
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun kasu gungu-gungu har daba biyar, su ka yi sansani-sansani a Dajin Rugu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Safana da Batsari, wasu kuma na a cikin Zamfara.
Majiya ta ce abin da ba su sani ba shi ne, ko ‘yan bindigar sun yi kaka-gida ne a wurin, ko kuma yada zango kawai su ka yi, su ɗan kwana biyu, sannan su yi gaba.
Mazauna yankunan sun roƙi Hukumar Sojoji da Gwamnatin Jihar Katsina su ɗauki matakan gaggawa, kuma su hana ‘yan ta’adda ɗin fara kai wa mazauna kusa ko nesa da su farmaki.
Ɗanƙarami da tawagar sa sun yi ƙaurin suna kai hare-hare a garuruwan Zamfara tare da kai wa sansanonin sojoji hari.
Wani shugaban jama’a a yankin wanda ba ya so a ambaci sunan sa, ya ce tuni wasu mazauna da dama sun tsere daga yankin don gudun kada bala’in ya ritsa da su.
Ya roƙi sojoji su yi amfani da sojojin sama da na ƙasa domin su ragargaje ‘yan ta’addar.
Su ma mazauna garin Runka sun koka cewa tun daga makon ya da ya gabata an ga maharan su na share dazuka su na kafa bukkoki, lamarin da ke nuna alamar sun je zama wurin ne dindindin.
“Mun ji an ce Ɗanƙarami ya je wurin Usman Moɗi-Moɗi har ya ba shi muggan makamai domin ya ƙara ƙarfi.
“Kuma shi ma Ɗankarami ɗin ya zo da na sa muggan makaman. To tawagar sa na da yawan da mazauna yankin su ka ce ba su taɓa ganin yawan ‘yan bindiga kamar su ba. Kuma ba su taɓa ganin muggan makamai kamar wanda su ka gani a wurin tawagar su Ɗanƙarami ba.”
An tuntuɓi Ibrahim Ahmad, Mashawarcin Harkokin Tsaro na Gwamna Aminu Masari, ya ce hukumomin tsaro ne kaɗai za su iya bayani kan lamarin.