Ƙungiya Miyetti Allah (MACBAN), Reshen Jihar Filato, ta kai kuka ga Gwamnan Jihar Filato da jami’an tsaro cewa ƙabilar Mwaghavul na cikin Ƙaramar Hukumar Mangu na gagarimin shirin kakkashe su ƙarƙaf a yankin.
Shugaban MACBAN na jihar, Muhammad Nura, ya aika wa Gwamna da shugabannin jami’an tsaron jihar wasiƙa cewa an sace masu shanu sama da 25,000.
Ya ce waɗannan shanu sama da 25,000, ko dai an karkashe su, ko kuma an sace su an yi wani lunguna da su.
Ya ce kuma dukkan shanun, ƙabilar Mwaghavul ne su ka sace su.
Ya ce an kai wa Fulanin yankin shiryayyen hare-hare ne a yankunan Bwoi, Kombun, Sarfal, Rinago, Jukga, Kuwes, Kaangag, Fari kasa, Kerana, Lugga, Dimeza, Fungong, Gindiri, Gok, Bughan Gida, Millet, Rufwang, Tidiu, Dejwak, Rufwang, Lupo, Wushik, Jwack, Chan da Hilltop.
Lamarin dai ya biyo bayan wani munmunan harin da wasu da ake zargi sun kai a yankin.
Ƙabilar Mangu ta yi zargin makiyaya sun kashe masu mutum 125. Amma dai jami’an tsaro sun tabbatar da kisan 85, sai jikkata 37.
An daɗe Fulani da kabilun yankin na kashe junan su.
Fulani sun yi kukan cewa ba a bari su ɗauki matattun su su yi masu sallah su rufe su.
“Babu abin takaici kamar ka ga ungulaye da karnuka na cin naman ɗan’uwan ka a dajin mangu.”
Ya ce an kwashe masu dubban shanu, tumaki, awaki, kaji, talotalo da agwagi. Kuma duk ƙabilar Mwaghavul ne su ka sace su. Wasu kuma sai watangarirya su ke a daji.
Sai dai ƙabilun yankin su ma sun yi kira ga Shugaban Miyetti Allah ya umarci makiyaya su daina kashe masu ƙabilun su.
Zargin Shirin Kai Masu Harin Ramuwar Gayya:
PREMIUM TIMES Hausa dai makonni biyu baya ta buga labari cewa makiyayan da ke maƙautaka da yankunan da aka kashe mutum 85 na fargabar kada a yi ramuwar-gayya a kan su.
Mazauna Rugar Gabɗo da dukkan su makiyaya ne, kuma su ke zaune a gefen yankunan da mahara su ka kashe aƙalla mutum 85 a ranar Talata, su na neman taimakon tsaro daga jami’an tsaro.
Sun bayyana cewa su na fargabar kada mazauna yankunan da aka yi kashe-kashen su kai masu harin ramuwar-gayya domin su huce haushin su a kan su.
Su dai mazauna yankunan da aka yi kashe-kashen a cikin Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato, sun yi zargin cewa wasu makiyaya ne su ka kai masu hari su ka yi masu kisan-gilla. Amma ba su ce makiyayan da ke cikin yankin su ne su ka mai masu harin ba.
Duk da cewa Jihar Filato ta saka dokar hana fita awoyi 24 daga safiya zuwa wata safiyar a yankin, tun a ranar Talata, domin gudun kai hare-haren huce haushi, waɗannan makiyaya sun ce su na cikin zaman ɗarɗar.
Makiyayan waɗanda ke Rugar Gabɗo sun ce a cikin kwanakin nan uku su na ganin gilmawar mutanen da ba kusa da su su ke ba, su na fitowa daga yankunan da aka yi kashe-kashe ne, su na sintiri a gefen rugagen su.
Sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa a ranar Alhamis da dare cewa su na tsoron kada a kai masu hari a cikin daren, idan dai gwamnati ba ta tura masu jami’an tsaro ba.
“Mu na kira ga jami’an tsaro su zo su ceci mu da ƙananan yaran mu da matan mu, waɗanda su ne lamarin zai fi shafa idan ya yi muni.
“Abin babu daɗi, jami’an tsaro na buƙatar su ƙara himma sosai, saboda ‘ya’yan mu ƙanana da matan mu na cikin matsala. Kowane lokaci za a iya kai masu hari cikin dare.” Inji Muhammad Gendero, wani mazaunin rugar.
Ya ce waɗanda harin zai iya shafa sun kai ɗaruruwan yara da mata.
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Filato, Alfred Alabo. Ya ce rundunar su za ta fitar da sanarwa a ranar Juma’a, dangane da rikicin.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa adadin rayukan waɗanda aka kashe ya kai 85, an tabbatar da rufe gawarwaki 57.
Kashe-kashen da su ka afku a ranar Talata a Ƙaramar Hukumar Mangu, an tabbatar da salwantar rayuka 85 a ƙauyukan Fungzai da Kubwat.
Shugaban Ƙungiyar Ƙabilar Mwaghavul na Ƙasa, Joseph Gwankat ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da ‘yan jarida, a ranar Laraba.
Ya gaba da manema labarai ɗin ne bayan taron da aka yi a fadar Basarake Mishkcham Mwaghavul na Mangu, John Hirse.
Har yanzu dai ‘yan sanda ba su fito sun bayyana adadin waɗanda aka kashe ba.
Shi kuma Gwankat ya ce ana ci gaba da neman mutanen da har yanzu ba a ji ɗuriyar su ba tukunna a cikin yankunan biyu da aka yi mummunan kisan.
Ya ce an kai wa ƙauyuka da dama hari, kuma duk kusan a lokaci a lokaci ɗaya.
Mazauna yankunan dai na zargin cewa makiyaya ne su ka yi kisan, kuma su ka riƙa banka wa bukkoki wuta da kuma lalata amfanin gona.
A lokacin taron da aka yi a fadar Basaraken Mangu, an ga mata sun fito har fadar su na cike da nuna fushi su na zanga-zangar lumana.
Cikin waɗanda su ka halarci taron akwai Mataimakin Gwamnan Filato, Soni Tyoden, shugabannin hukumomin tsaro, dagatai da jami’an gwamnati daban-daban.
Hirse, Shugaban Ƙaramar Hukuma da Hakimai sun roƙi a ƙara yawan jami’an tsaro a yankunan.
Zuwa lokacin haɗa labarin dai an binne gawarwaki 57 a safiyar Laraba ɗin nan.
Discussion about this post