Gamayya ko ‘majar’ ‘Yan Majalisar Wakilai na Ƙasa waɗanda za su yi wakilci daga 2023 zuwa 2027, daga jam’iyyu takwas, sun amince su kiyaye da bin tsarin karɓa-karɓa da APC ta shigo da shi a shugabancin majalisar.
Sun amince da sharuɗɗan karɓa-karɓa ɗin a ranar Talata, yayin da su ke ƙaddamar da gangamin ‘maja’ ɗin da su ka yi, wadda su ka raɗa wa sunan Turanci, “Join Task”, a Abuja.
An haɗa mambobin maja ɗin daga jam’iyyu takwas da su ka haɗa da APC, PDP, LP, NNPP, APGA, SDP, ADC, da YPP.
Sai dai kuma ba dukkan mambobin majalisar kakaf ba ne su ka amince da shiga wannan majar.
Da ya ke magana lokacin ƙaddamar da maja ɗin su, Honarabul Bello Kumo, ɗan APC daga Gombe, ya ce har yanzu mambobin maja ɗin ba su da ɗan takarar da su ke goyon baya. Amma su na jiran su ga tsarin karɓa-karɓar da APC, jam’iyya mai mulki kuma mafi rinjaye a majalisa za ta fitar.
“Mu saƙon mu ga ga ‘yan Najeriya a daidai wannan lokaci shi ne, a shirye mu ke domin mu yi aikin bunƙasa ƙasa da inganta rayuwar mu.
“Idan kuwa mu na son cimma wannan kyakkyawan ƙudiri na mu, to kenan tilas sai mun yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ɓangaren Zartaswa na Gwamnati, amma kuma ba tare da sun yi watsi da ‘yancin mu na masu doka ba kuma masu ‘yancin su.
“Mu dai abin da ya fi damun mu shi ne haɗin kan ƙasar nan da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali sai kuma nagartar Majalisa ta 10. ”
Shi ma Aliyu Madaki, ɗan NNPP da Kano, ya ce mambobin majalisa ba za su zama gugar-yasa ga ko ma wane ne zai zama Kakakin Majalisa ba. Amma dai kawai su na bai wa APC dama ce su fitar da shugabanni bisa tsarin da duniya ta fi gamsuwa da shi.
Ya ce dama ko’ina a dimokraɗiyya, ana bai wa jam’iyyar da ta fi rinjaye damar fitar da shugabannin majalisa.
“Ni da na fito daga jam’iyyar adawa, za mu yi adawa sosai, amma ba bisa son kai ba. Zan yi adawa ne domin mu wanzar da abin da zai kawo wa ƙasar nan ci gaba mai mai albarka.”
APC na da wakilai 177, PDP 116, LP 38, NNPP 19. APGA na da 5, ADC 2, SDP 2, sai kuma YPP 1.
Yayin da Kumo na Gombe ne shugaban maja, Kingsley Chinda na PDP daga Ribas ne shugaba na biyu. Sai Ali Madaki na NNPP daga Kano ke Sakataren maja.
Discussion about this post