Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce abin damuwa ne matuƙa ganin yadda kashi 70 bisa 100 na Sanatoci 109 da Mambobin Tarayya 360 da ke tare da shi, ba su ci zaɓen 2023 a ƙoƙarin su na ci gaba da zama majalisa ba.
Lawan ya nuna wannan damuwar a ranar Alhamis, yayin buɗe Ofishin dindindin na Cibiyar Nazarin Majalisa da Dimokraɗiyya ta Ƙasa (NILDS), a Abuja.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya buɗe mazaunin dindindin na NILDS ɗin.
Da Lawan ke jawabi, ya nuna rashin jin daɗin yadda al’ummar da ‘yan majalisar su ka yi fatali da su, su ka ƙi sake zaɓen su a 2023.
Ya ce daga cikin abin da za su yi domin ganin su rage yawan sauya ‘yan majalisa shi ne a shirya tsare-tsaren da za su inganta ayyuka da gudummawar ‘yan majalisa.
“Abin takaici ne da muka rasa kashi 70 bisa 100 na Sanatoci da Mambobin Tarayya waɗanda talakawa su ka ƙi sake zaɓen su. Don haka abin da za mu yi domin rage ci gaba da faruwar haka, shi ne mu shirya wa sabbin da za su shigo yanzu wasu tsare-tsaren inganta su.”
Daga nan ya shawarci jama’a da kuma ‘yan majalisa su yi rajista da NILDS domin ƙarin ilmin aikace-aikacen majalisa.
Lawan ya jinjina wa Shugaba Buhari bisa ƙoƙarin da ya ce ya yi na kafa cibiyar.
Idan za a iya tunawa, shi ma Lawan ana kuka da yadda aka yi ya sake cin zaɓe, bayan kotu ta haramta takarar sa.
Hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke wanda ta maida masa takarar sa, zai zama ɗaya daga cikin shari’a saɓanin hankalin da ya taɓa faruwa a Najeriya.
Cikin sanatocin da ba za su koma Majalisa ba, har da Kabiru Gaya na Kano, ɗan APC, wanda Kawu Sumaila na NNPP ya kayar da shi.
Discussion about this post