Sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya kori dukkan jami’an gwamnatin da tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje ya naɗa.
Gwamna Abba ya fitar da Doka ta Musamman, wadda ya bayyana korar duk wani da Ganduje ya yi wa naɗin siyasa, musamman shugabannin Hukumomin Gwamnati da kamfanoni.
Ya kuma rushe hukumomin gudanarwar dukkan kamfanoni da cibiyoyi da manyan makarantu.
Wannan umarni ya shafi duk wani naɗin da Ganduje ya yi na siyasa wanda ke da adadin lokacin sauka da waɗanda ma wa’adin saukar su bai yi ba.
Abba ya umarci jami’an tsaro su karɓe duk wasu kadarorin gwamnatin Jihar Kano, waɗanda aka sayar a lokacin mulkin Ganduje.
“Ina sanar da cewa a yau duk wasu wurare mallakar gwamnatin Kano da aka sayar ko aka kaɗas a mulkin Ganduje, to daga yau gwamnati ta ƙwace kayan ta.
“Ina kira ga DSS, ‘yan sanda, Sibil Difens da Hisbah su kula da wuraren kafin a ji hukuncin da gwamnatin Kano za ta ɗauka.”
“Dukkan filaye da fegunan da aka sayar mallakar makarantu, wuraren ibada ko al’adu, asibitoci da maƙabartun da aka sayar, to gwamnati ta ƙwace. Haka ma duk wani gini da aka yi a jikin badala ko ganuwa, shi ma an ƙwace, in dai a cikin filin gwamnatin Kano aka yi ginin.”
Ya ce za a kafa kwamitin bincike domin a tabbatar an hukunta masu hannu wajen yin watanda da kadarorin gwamnatin Jihar Kano.
Haka nan an kafa Hukumar Tsaftace Mullahi wadda ya ce nan ba da daɗewa ba zai ƙaddamar da ita.
A wani labarin kuma, Abba ya naɗa Baffa Bichi sabon Sakataren Gwamnatin Jiha, sai Kakakin sa Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ma ya zama Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna.
Discussion about this post