Tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya bayyana cewa sai ya ga abin da ya ture wa buzu naɗi a takarar shugaban majalisar dattawa da ya le yi.
Yari na daga cikin na gaba gaba da ke neman zama shugaban majalisar dattawa, sai dai kuma babban ƙalubalen dake gaban sa shine yadda yayi hannun riga da jam’iyyar sa ta APC wacce ta zaɓi Godwill Akpabio a matsayin ɗan takaran ta.
Daya ke tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, Yari ya ce ” Ba dani za ayi ɗauki ɗora ba, ban san maganar Akpabio ba saboda haka da ni za a fafata wajen neman kujerar shugabancin majalisar dattawa, ba zan janye ba.
Jam’iyyar APC ta tsaida Akpabio da Barau Jibrin a matsayin ƴan takarar ta na shugaban majalisar dattawa da na mataimakin shugaban majalisa.
Wasu da ga cikin ƴan takarar har da shi kansa Yari sun yi watsi da wannan tsari na jam’iyyar APC na kai shugabancin majalisar yankin Kudu.
” Dokar kasa ita ce kan gaba, kuma da ita nake tunkaho, babu wani ko wasu da zasu hanani neman abinda dokar kasa ta bani damar nema.
” Ni cikakken dan jam’iyya ne babu wani da ya gaya min wai an kai kujerar shugaban majalisar dattawa yankin kudu ne. Saboda haka kowa zai fito ne ya nema kamar yadda doka ta ce.
” Sanatoci da dama sun tattauna da ni kuma sun bani goyon baya suna tare da ni. Ba zan basu kunya ba saboda haka sai naga abinda ya ture wa buzu nadi.