Ɗaya daga cikin ‘ya’yan tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, mai suna Olujonwo Obasanjo, ya bayyana goyon bayan sa ga tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ta 10.
Olujonwo wanda jigo ne shi ma a cikin APC, ya kuma bayyana cewa ya na goyon bayan Tajuddeen Abbas ya zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Yayin da ya ke ganawa da manema labarai, ranar Asabar a Abuja, Olujonwo ya yi roƙo da kuma kira ga Sanatoci da Mambobin Tarayya su zaɓi Akpabio da Abbas a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa da kuma Kakakin Majalisar Tarayya.
Ya ce Akpabio ya cancanta, domin ya nuna tsantsar biyayya ga jam’iyyar APC da kuma ɗa’a ga Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
“Sanata Godswill Akpabio sai da ya kashe maƙudan kuɗaɗen sa, ya fito takarar zaɓen fidda gwani. Amma kuma ana gobe zaɓen ya fito ya ce ya janye wa Bola Tinubu.”
Da ya ke magana kan Abbas kuma, ɗan na Obasanjo ya ce shi ma Abbas ɗin ya cancanci zama Shugaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Tuni dai Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya ce Tinubu ba zai tafka irin kurakuren da Jonathan da Buhari su ka tafka ba.
Ya bayyana haka ne yayin da ya ke faɗin dalilin da ya sa APC da Tinubu su ke goyon bayan Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, shi kuma Tajuddeen ya zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta kauce daga maimaita irin kurakuren da gwamnatocin Jonathan da Buhari su ka tafka wajen zaɓen shugabannin Majalisar Tarayya.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, inda ya tunatar da rikicin da ya haddasa Mambobin Majalisar Tarayya su ka zaɓi wanda ba shi jam’iyya ke so ba.
Ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya yi sakacin kasa iya riƙe ragamar mulkin sa tun a ranar Aminu Tambuwal ya zama Kakakin Majalisar Tarayya. Ya ƙara da cewa wannan lamari ne ya ƙara zama dalilin faɗuwar PDP a zaɓen 2015.
Shettima ya ce shi kuma Shugaba Mai Barin Gado, Muhammadu Buhari, ya kasa samun gagarimar nasara a shekaru huɗun sa na farko, saboda an zaɓi shugabannin majalisa waɗanda ba su ne jam’iyyar APC ke so ba.
Shettima ya bayyana haka yayin ganawar sa da Tajuddeen Abbas da Ben Kalu, waɗanda su ne APC da Tinubu ke so su zama Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.
An yi ganawar tare da gungu ko gamayyar mambobi masu biyayya ga zaɓin da jam’iyya ta bayar a batun shugabancin Majalisa.
Tuni dai mambobin da ba su goyon bayan Abbas da Ben Kalu, sun kafa ƙungiya, COPSA, wacce a ƙarƙashin ta su ke ta faɗa da Abbas da Ben Kalu da kuma uwar jam’iyya, APC.
Daga cikin masu adawa da Abbas, har da Mataimakin Kakakin Majalisa, Idris Wase, Shugaban Masu Rinjaye, Alhassan Doguwa, Sada Soli, Miriam Onuoha da Muktar Betara.
Dangane da wannan karankatakaliya, Shettima ya ce ya na magana da dukkan hasalallun ‘yan takarar, domin a cimma sasanta saɓanin.
“Zan yi ƙoƙari na ga na tuntuɓi dukkan sauran masu takara. Shi dai Honorabul Betara ɗan uwa na ne. Daga yanki ɗaya mu ka fito, kuma daga jiha ɗaya mu ka fito. Kuma akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin mu. Na gana da shi makonni biyu da su ka gabata. Zan kuma ci gaba da lallashin sa,” cewar Shettima.
Wajen ƙarfe 1 na yamma a yau kuma na gana da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya, Idris Wase. Za mu ci gaba da tuntuɓar juna.”
“Lokacin da Obasanjo ya rasa ta-cewa a majalisa, ai kowa ya shaida yadda zangon sa na farko ya kasance bai yi abin kirki ba. Saboda ruɗanin da aka riƙa yi. Ba don komai ba saboda Obasanjo ya yi sakaci Aminu Tambuwal ya zama Kakakin Majalisar Tarayya a lokacin.
“A yanzu ita ma Mariam Onouha akwai shaƙuwa tsakani na da ita. Zan tuntuɓe ta.”
Discussion about this post