Ɗan takarar da ke sahun gaban neman shugabancin Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa a yanzu sanatoci 85 su na goyon bayan sa.
Ya ƙara da cewa yawan masu goyon bayan na sa za su ƙaru zuwa 85 ko 86 yayin da aka zo zaɓe cikin watan Yuni.
Akpabio wanda shi APC da Gwamnonin APC da kuma Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ke goyon baya, ya ce ya na da yaƙinin lashe zaɓen cikin gida na zama shugaban majalisar dattawa.
Ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, lokacin da ya ja zugar tawagar sa, su ka kai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ziyara.
Ya ce zaɓaɓɓun sanatocin da ke goyon bayan sa, duk mutane ne nagari, waɗanda su ka kawar da kan su daga siyasar kuɗi.
“Ran ka ya daɗe, ina tabbatar maka mutanen nan da ke tare da ni, mutanen kirki ne, waɗanda su ka kau da idanun su daga nairori da daloli.”
A ƙarshen makon jiya ne dai Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashin Shettima ya ce, “Tinubu Ne Ya Ce Bai Yarda A Zaɓi Musulmi Ba, Sai Dai Kirista Tilas.”
Kashin Shettima, Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya bayyana dalilin da ya sa APC, Tinubu da shi kan sa su ka yanke shawarar amincewa Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Ya ce Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ne ya yi zurfin tunani da hangen nesa cewa kada Musulmi ya yi Shugaban Majalisar Dattawa.
Da ya ke wa Tajuddeen Abbas da tawagar sa bayani yayin da su ka kai masa ziyara a ranar Juma’a, Shettima ya ce sun fahimci bai kamata a ce Shugaba da Mataimaki da Kakakin Majalisa duk Musulmi ba ne, sannan kuma a ce Shugaban Majalisar Dattawa shi ma Musulmi ne ba.
Haka kuma ya ce Tinubu ba zai tafka irin kurakuren da Jonathan da Buhari su ka tafka ba – Shettima
Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta kauce daga maimaita irin kurakuren da gwamnatocin Jonathan da Buhari su ka tafka wajen zaɓen shugabannin Majalisar Tarayya.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, inda ya tunatar da rikicin da ya haddasa Mambobin Majalisar Tarayya su ka zaɓi wanda ba shi jam’iyya ke so ba.
Ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya yi sakacin kasa iya riƙe ragamar mulkin sa tun a ranar Aminu Tambuwal ya zama Kakakin Majalisar Tarayya. Ya ƙara da cewa wannan lamari ne ya ƙara zama dalilin faɗuwar PDP a zaɓen 2015.
Shettima ya ce shi kuma Shugaba Mai Barin Gado, Muhammadu Buhari, ya kasa samun gagarimar nasara a shekaru huɗun sa na farko, saboda an zaɓi shugabannin majalisa waɗanda ba su ne jam’iyyar APC ke so ba.
Shettima ya bayyana haka yayin ganawar sa da Tajuddeen Abbas da Ben Kalu, waɗanda su ne APC da Tinubu ke so su zama Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.
An yi ganawar tare da gungu ko gamayyar mambobi masu biyayya ga zaɓin da jam’iyya ta bayar a batun shugabancin Majalisa.
Tuni dai mambobin da ba su goyon bayan Abbas da Ben Kalu, sun kafa ƙungiya, COPSA, wacce a ƙarƙashin ta su ke ta faɗa da Abbas da Ben Kalu da kuma uwar jam’iyya, APC.
Daga cikin masu adawa da Abbas, har da Mataimakin Kakakin Majalisa, Idris Wase, Shugaban Masu Rinjaye, Alhassan Doguwa, Sada Soli, Miriam Onuoha da Muktar Betara.
Dangane da wannan karankatakaliya, Shettima ya ce ya na magana da dukkan hasalallun ‘yan takarar, domin a cimma sasanta saɓanin.
“Zan yi ƙoƙari na ga na tuntuɓi dukkan sauran masu takara. Shi dai Honorabul Betara ɗan uwa na ne. Daga yanki ɗaya mu ka fito, kuma daga jiha ɗaya mu ka fito. Kuma akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin mu. Na gana da shi makonni biyu da su ka gabata. Zan kuma ci gaba da lallashin sa,” cewar Shettima.
Wajen ƙarfe 1 na yamma a yau kuma na gana da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya, Idris Wase. Za mu ci gaba da tuntuɓar juna.”