Zaɓaɓɓun sanatocin APC sun gana da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas.
Tinubu ya kai ziyarar kwanaki biyu ce inda ya buɗe wasu ayyukan raya jiha da Gwamna Nyesom Wike ya gayyace shi buɗewa.
Zaɓaɓɓun sanatocin dai sun gana da Tinubu ne a ranar Alhamis. Daga cikin waɗanda su ka gana da Tinubu, akwai tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, Shuaibu Salisu daga Ogun, Solomon Olaminekan daga Legas, sai kuma wasu da dama.
Ba a dai san abin da su ka tattauna ba, amma dai wani bidiyo ya nuna Akpabio na gabatar da sunayen sanatocin ga Tinubu.
An nuno Tinubu na gaisawa da kowane daga cikin su.
Ana ci gaba da zafin neman shugabancin Majalisar Dattawa, inda mutum shida ke nema wurjanjan.
Shida ɗin sun haɗa da Godswill Akpabio, Jibrin Barau, Abdul’aziz Yari, Gwamna Dave Umahi, Orji Uzor Kalu da Sani Musa.
A na su ɓangaren kuma, Gwamnonin APC sun ce Akpabio ne zaɓin su. Sun faɗi haka ne bayan wata ganawa da su ka yi.
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bada sanarwar cewa gwamnonin jam’iyyyar APC sun yanke shawarar amincewa su zaɓi shugaban majalisar dattawa daga yankin Kudu maso Kudu.
Dama kuma a baya sun ce ko dai ya shugaban majalisar dattawa ɗin ya fito daga Kudu maso Gabas ko kuma ya fito daga Kudu maso Kudu.
Sun kuma yarda cewa muƙaman shugaban masu rinjaye da mataimakin masu rinjaye da kuma bulaliyar majalisa, a bayar da su ga ‘yan takarar da aka roƙa su ka janye.
Sai dai kuma a cikin wani bidiyo da aka datso daga gidan talabijin na AIT, an nuno Ganduje ya tabbatar da cewa gwamnonin APC sun amince a zaɓi tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, domin ɗan yankin Kudu maso Kudu ne.
A cikin bidiyon an nuno Ganduje tare da wasu gwamnoni ciki har da Ben Ayade na Kuros Riba a wurin taro da wasu mutane.
Ganduje ya ƙara tabbatar da cewa babu abin da zai canja tsarin raba muƙaman majalisar dattawa da na majalisar tarayya zuwa shiyya-shiyya, kamar yadda su gwamnonin su ka tsara.
“Shugaban Majalisar Dattawa mun yarda a bai wa ɗan Kudu maso Kudu. Kuma tsohon gwamnan Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio mu ke so a bai wa.” Inji Ganduje.