Zaɓaɓɓen Sanata Osita Izunaso, ya ce lokacin da zai zama shugaban majalisar dattawa fa ya yi, don haka shi ya kamata ya yi shugabancin ba wani ba.
Saboda haka ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da shugabannin APC su warware mubaya’ar su daga kan Sanata Godswill Akpabio, sannan su naɗa a kan sa.
Ya ce idan za a yi adalci, to ya kamata a duba irin gudummawar da ya bai wa jam’iyyar APC, tun bayan kafuwar ta mataki-mataki, har zuwa yau.
Zaɓaɓɓen sanatan ya jaddada hakan a lokacin da ya ke Babban Cocin Ƙasa da ke Abuja, lokacin da aka yi taron addu’o’in samun nasarar wannan sabuwar gwamnati.
Taron dai na gamayyar shugabannin ɗariƙun Kiristoci ne bai-ɗaya.
Izunaso wanda shi ne tsohon Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa na APC, ya ce shi ne mafi cancantar zama Shugaban Majalisar Dattawa, idan aka auna gagarimar gudummawar da ya bai wa jam’iyyar APC.
Baya ga Izunaso da Godswill Akpabio, sauran sanatocin da ke neman shugabancin sun haɗa da Abdul’aziz Yari (Zamfara), Orji Uzor Kalu (Abiya), Sani Musa (Neja) da kuma Patrick Ndubueze (Imo).
Izunaso ya ce da shi aka kafa APC, kuma ya sadaukar da ƙarfin sa, lokacin sa domin ganin APC ta kai inda ta kai a yanzu.
Ya ce a farkon kafa jam’iyyar lokacin da ba ta da wani kwarjinin cin zaɓe, ya na cikin waɗanda su ka jure su ka ci gaba da rike jam’iyyar da daɗi, ba daɗi, komai wuya komai daɗi.
“Da ni aka kafa APC. Sai da mu ka shafe watanni shida a jere duk sati mu na zuwa Legas taro domin kafuwar APC, don a samu sunan da za a sa mata, kuma a tabbatar da kafuwar ta.
“Mu mu ka tsara tutar, mu ka riƙa tattaro kan jama’a daga cikin ‘yan adawa su na shigowa kafin ma mu kai ga yi mata rajista a CAC.
“Gwamna Fashola na nan da ran sa a yau ɗin nan, ya san duk abin da na ke faɗa, saboda tun daga ranar farko da shi aka fara komai.
“Mu ne mu ka tsara zaɓen fidda gwani na gwamnonin jihohi 36, kuma ba a samu inda aka kai ƙarar ko da ɗan takara ɗaya ba a kotu. Saboda me, saboda mun tsara abin da ya dace. Saboda haka za ku iya yarda da ni cewa wannan shi ne abin da ake kira cancanta.
“Mu ne sahun gaban kokawa da shugaban da ke kan mulki a 2015. Kuma mun yi nasara kan idon ku. Don haka idan har zan iya riƙe jam”iyya a lokacin, to don me ba za a ba ni shugabancin Majalisar Dattawa ba?”
“Don haka ni dai a yanzu a rama min wahalar da na yi wa APC, a saka min da shugabancin Majalisar Dattawa.” Inji Izunaso.
Discussion about this post