Manyan da ke sahun gaba a Majalisar Tarayya, kuma masu takarar shugabancin majalisar, sun ce ba su amince da wanda Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu da APC ke so ya zama Kakakin Majalisar Tarayya ba.
Tinubu da APC dai sun nuna goyon bayan su ga Tajuddeen Abbas daga Kaduna da kuma Ben Kalu daga Abiya.
Sai dai kuma Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Idris Wase, Tijjani Betara, Barau Jibrin, Sada Soji da Jaji duk sun ki amincewa da tsarin da Tinubu da APC su ka fito da shi.
Wase ne ya bayyana wannan matsaya ta su a ranar Litinin a otal ɗin Hilton, wurin ƙaddamar da takarar Muktar Betara, a Abuja.
Wase ya ce su biyar ɗin su yanke shawarar tafiya tare cikin haɗin kai domin su yi fatali da zaɓin da Tinubu da APC su ka yi.
Sauran inji shi sun haɗa Sada Soli, Alhassan Doguwa, Ahmed Jaji da Muktar Betara.
Betara dai ya fito jihar Borno, inda Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya fito.
Shi kuma Doguwa, ya na fuskantar tuhuma a kotu, bisa zargin kisan ‘yan adawa lokacin zaɓen majalisar tarayya a mazaɓar sa ta Doguwa/Tudun Wada, Kano.
A wurin taron ƙaddamar da Betara, cincirindon ‘yan majalisar da ke wurin sun riƙa fitowa fili su na nuna goyon bayan su ga waɗannan biyar ɗin, tare da nuna rashin goyon bayan Tajuddeen Abbas wanda Tinubu da APC ke so.
Yusuf Gagdi da Miriam Onuoha su ma sun halarci taron, amma dai su ba su fito sun ƙalubalanci Tinubu da APC ba.
Wase ya ce bai goyi bayan duk wata matsayar da su Tinubu da APC su ka ɗauka ba tare da tuntuɓar majalisa ba.
A ƙarshen makon jiya ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Tinubu ya ‘yarda’ Tajuddeen Abbas ya zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Alamomi masu ƙarfi kuma tabbatattu na nuna cewa Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya amunce Honorabul Tajuddeen Abbas daga Jihar Kaduna ya zama Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, wato Majalisar Tarayya.
Haka kan kuma ya amince Ben Kalu daga Abia ya zama Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.
Idan hakan ta tabbata, to yankin Arewa ta Tsakiya ya tashi a cikin ‘yan-kalar-dangi kenan, ta yadda dukkan muƙamai shida bai samu ko ɗaya ba.
Tinubu ya amince da Abbas a wani taron da aka yi a ranar Juma’a da rana, a gidan da Gwamnatin Tarayya ta zaunar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, wato Defence House, da ke Maitama, Abuja.
Ben Kalu, wanda ɗan majalisa ne daga Jihar Abiya, q yankin Kudu maso Gabas, an ɗauko shi ne domin a saisaita giɓin yankin na su.
Alamomi kuma sun nuna cewa Tinubu ya amince tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya kasance Shugaban Majalisar Dattawa, shi kuma Barau Jibrin daga Kano ya zama mataimakin sa.
An ɗauki Barau daga Arewa maso Yamma, yankin da Shugaban Ƙasa mai barin gado, Buhari ya fito.
Tunda Shugaba ya fito daga Kudu maso Yamma, mataimakin sa daga Arewa maso Gabas, Kakaki daga daga Arewa maso Yamma, Shugaban Majalisar Dattawa daga Kudu maso Kudu, sauran muƙamai da su ka rage kuma za a raba su cikin sauran shiyyoyi kenan.
A kula cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya zai fito daga Kudu maso Gabas kenan, idan aka tafi a kan wannan yarjejeniya.
Takarar Shugabancin Majalisar Tarayya: ‘Ba Zan Janye Wa Kowa Ba’: Hasalallen ɗan takara daga Arewa ta Tsakiya:
Wani ɗan takara daga Arewa ta Tsakiya da ya nemi a sakaya sunan sa, ya shaida wa wakilin mu cewa ba fa zai janye wa kowa takarar da ya ke yi ba.
Ya ce ya tuntuɓi shugabannin LP da Rabi’u da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da wasu, kuma duk sun ba shi tabbacin zai yi nasara a zaɓen Kakakin Majalisa da za a yi a ranar 13 Ga Yuni.