Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila shi da Zaɓaɓɓen Sanatan Akwa Ibom, Godswill Akpabio, sun gargaɗi zaɓaɓɓun ‘yan majalisa cewa a kul su ka bari saɓani da ƙiyayya su ka shiga tsakanin su da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa.
Sun ce idan su ka yi tawaye ga waɗanda APC ke so su yi shugabanci a Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya, to fa sun buɗe ƙofar shiga saɓani kenan tsakanin majalisa da shugaban ƙasa.
Su biyun sun bayar da wannan gargaɗi a ranar Laraba, a wurin wani taron da su ka yi da zaɓaɓɓun ‘yan majalisar tarayya, a otal ɗin Hilton, Abuja.
Akpabio wanda tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom ne a zamanin Umaru da zamanin Jonathan, ya yi sanata daga baya. Sannan kuma ya koma APC, inda Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi Ministan Harkokin Neja Delta.
Akpabio shi APC da Tinubu ke so ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Shi kuma Tajuddeen Abbas wakilin tarayya daga Jihar Kaduna, shi su ke so ya zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Sai dai kuma wasu masu takarar muƙaman sun ƙi amincewa su janye masu.
Da ya ke tuna abin da ya faru a baya, Gbajabiamila ya bayyana cewa ya na da-na-sanin goyon bayan da ya yi wa Aminu Tambuwal ya zama Kakakin Majalisar Tarayya cikin 2011, ba tare da son ran Shugaba Goodluck Jonathan na lokacin ba.
A lokacin Gbajabiamila shi ne Shugaban Masu Rinjaye, kuma shi ya ja zugar goyon bayan Tambuwal da Mataimakiyar sa, Mulikat Akande.
Yayin da rigimar ke neman ta yi tsami, ɗaya daga cikin masu takarar, wato Gagdi, ya ce wa Tinubu Kaduna ba ta cancanci ta fito da Kakakin Majalisar Tarayya ba.
Ɗan Majalisar Tarayya wanda kuma ke sahun gaba na masu adawa kan batun fito da Kakakin Majalisar Tarayya, Yusuf Gagdi, ya bayyana cewa rashin adalci ne tantagarya da APC ta bayar da shugabancin majalisar tarayya ga jihar Kaduna.
Discussion about this post