Wannan ce rana ta karshe na bikin ma’aikata da gwamnatin Buhari ta yi, kwanaki kadan suka rage wannan gwamnati ta kawo karshe.
Duba da yadda al’amura suka faru tsakanin gwamnatin Buhari da Yan Kwadago a tsawan wannan lokacin, shin za a ce akwai yabo?
Duk da cewar kungiyoyin Ma’aikata dama masu gwagwarmayar kwadago a Nijeriya kashi kadan ne, basu kai kashi 30 ba na yawan ma’aikata a Nijeriya.
Akwai miliyoyin Yan Kwadago masu aikin karfi da kwararru wanda su ke aiki a kananan masana’antu da daidaikun alm’ummah masu hannu da shuni da ke cikin tasku a wajen da suke aiki, ba a ma tasu wajen nema musu haki da mafita.
Tsakanin Ma’aikata da Gwamnatin Buhari, banda zanga zanga a kan kari da cire tallafin Man Fetur da a ka sha fama da Gwamnatin, babban lamari shine batun karin albashi.
Gwamnatin Buhari ta dau tsawan lokaci kusan shakaru uku kafin ta kara albashi daga dubu 18 zuwa dubu 30, da kuma tsari motsa albashin wasu ma’aikatan kadan wato consequential adjustment, wanda wani sabon salo ne da Gwamnatin ta bullo da shi, wanda wannan baiyi wa ma’aikatan dadi ba.
Ba kawai Kungiyoyin Kwadagon ba, hatta masana da ita kanta Gwamnatin bata gamsu cewa karin albashi da akayi ba zai daidaita da yanayin matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kaya ba a Nijeriya.
Wannan tunani na Gwamnatin ne ya sanya ta fito da wani alawus don karawa wasu bangare na ma’aikatan ta albashi.
A wani bangare, anga yadda a ka shafe tsawan wata 8 Malaman Jami’a da Ma’aikatan Jami’ar suka shafe suna yajin aiki, har yanzu wannan rigima bata kare ba, har yanzu maganar ma tana gaban Kotu. Gwamnatin Buhari ta ki biyan su albashin da ya kai tsawan wata takwas.
Hatta Kungiyoyin ma’aikatan Lafiya da wutar lantarki suma suna cikin danbarwa da Gwamnatin a kan wasu alkawura da Gwamnatin ta gaza cimmawa.
Ko shugabannin ASUU sun yi nuni da cewar ba a taba samun gwamnati da bata san darajar ma’aikata kamar Gwamnatin Buhari. Su kansu shugabannin Kungiyoyin Kwadagon ma sun koka a kan rashin cika alkawari daga wurin Gwamnatin duk lokacin da aka shiga yarjejeniya da ita.
Duk da haka ma fa, ba a maganar sauran ma’aikatan da ba a Gwamnati suke ba, wayanda su sukafi yawa, kuma su suke cikin mawuyacin hali, wajen karancin albashi, kora ba bisa ka’ida ba, da musgunawa kala kala.
Duk da cewar wannan Gwamnatin ta yi karin alawus ga wasu rukunin ma’aikatan ta, kuma ta janye aniyar ta cire tallafin Man Fetur, wannan bai isa gamsar da ma’aikatan Nijeriya ba a kan matsalolin ma’aikata ba.
Tabbas wannan Gwamnatin tafi Gwamnatocin baya gazawa a kan samawa ma’aikata walwala.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post