Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya nemi Kotun Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta ɗage zaman sauraren ƙarar da ya shigar kan nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023.
Lauyan Obi mai suna Awa Kalu ne a shaida wa mambobin shari’ar ƙarar na Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ɗin su biyar, bisa jagorancin Babban Mai Shari’a Haruna Tsammani, a ranar Laraba.
Lauyan Obi ya ce ya nemi a ɗage zaman shari’ar saboda wani abin da ya faru, wanda ba a yi zaton haka zai faru ɗin ba.
Saboda haka ne Obi ya nemi a ɗage zaman sauraren ƙarar zuwa ranar Alhamis.
Kalu wanda Farfesa ne a fannin shari’a kuma babban lauya (SAN), ya bayyana cewa biyu daga cikin zaƙaƙuran lauyoyin da ta ke ƙarƙashin tawagar su lauyoyin Peter Obi ɗin, ba su da lafiya. Saboda haka ya roƙi a ɗage ci gaba da sauraren ƙarar sai washegari Alhamis.
A ranar Litinin ce dai Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta karɓi kwafen takardun zargin Asiwaju da Peter Obi ya yi cewa Tinubu ya yi harƙallar muggan ƙwayoyi.
Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa da ke Abuja ta karɓi kwafen takardun da aka shigar, waɗanda ake kafa hujja da su cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi tu’ammali da muggan ƙwayoyi, har Amurka ta ci shi tarar dala 460,000.
Kotun ta karɓi takardun a matsayin shaidu a ƙarar da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na LP ya shigar.
Obi ya na ƙalubalantar nasarar Tinubu, inda ya ke neman kotu ta ayyana cewa shi ne ya ci zaɓe, ko kuma a soke zaɓen, a yi wani sabo baki ɗaya.
Obi ya na ƙarar cewa an tafka maguɗi a lokacin zaɓe, sannan kuma Tinubu bai cancanci tsayawa takarar zaɓe ba.
An dai rantsar da Tinubu a ranar Litinin, duk kuwa da cewa ana ci gaba da shari’ar da Obi, Atiku da APM su ka maka shi.
Za a kammala shari’un a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a cikin Satumba, kafin daga nan a rankaya Kotun Ƙoli.
Obi ya kafa wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa hujja daga dala 460,000 da Kotun Gundumar Illinois ta ci Tinubu tara, bayan kama shi da muggan ƙwayoyi a Amurka.
Wannan kwafen shaida dai shi ne mai lamba 93C 4483 da ke gaban alƙalan kotun, ƙarƙashin jagorancin Babban Mai Shari’a, Haruna Tsammani.
Haka kuma Obi ya ce takarar Kashim Shettima haramtacciya ce, domin ya fito takara wuri biyu a lokaci guda. Wato takarar sanatan Barno da kuma takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Discussion about this post