Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya jaddada cewa a halin yanzu Najeriya na buƙatar haziƙi kuma mai kishi irin Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, domin bunƙasa ƙasar nan baki ɗaya.
Tinubu ya yi wannan jawabi a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, inda ya kai ziyarar buɗe ayyuka bisa gayyatar Gwamna Nyesom Wike na Jihar.
Tinubu ya ce duk da Jihar Ribas ba jihar APC ba ce, gwamnatin sa ba za ta watsar da kowace jiha ko yanki ba, za ta yi adalci sosai wajen yi wa kowane yankin ƙasar nan ayyukan bunƙasa ƙasa da tattalin arziki baki ɗaya.
Tinubu ya buɗe gadar sama ta 12 da Wike ya gina a Fatakwal, cikin shekaru takwas na mulkin sa.
A wurin buɗe gadar ta Rumuokwuta, Tinubu ya ce gwamnatin sa mai hawa ranar 29 Ga Mayu za ta bar gadon manyan ayyukan raya ƙasa da bunƙasa tattalin arziki a faɗin yankunan ƙasar nan.
A jawabin sa,Gwamna Wike ya ce ya gayyaci Tinubu ne a matsayin cika alƙawarin da ya ɗaukar wa Tinubu a lokacin kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa, inda ya shaida wa Tinubu a Ribas cewa, idan ya ci zaɓen shugaban ƙasa, to zai gayyace shi buɗe wasu ayyukan raya jiha da ya gina.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa APC ta nesanta kan ta da ziyarar da Tinubu zai kai wa Gwamna Wike a Ribas.
Jam’iyyar APC Reshen Jihar Ribas ta nesanta kan ta daga ziyarar buɗe manyan ayyukan raya jiha da Gwamna Nyesom Wike ya gayyaci Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Tinubu ya amsa gayyatar ziyarar kwanaki biyu a Ribas domin ya ƙaddamar da gadar sama da gine-ginen kotu waɗanda Gwamna Nyesom Wike ya yi.
Tuni dai Wike ya bayyana cewa yau Laraba ranar hutu ce, kuma ya yi kira ga jama’a a fito a yi tururuwar tarbar Tinubu
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran APC na Jihar Ribas, Darlington Nwauju ya fitar, ya ce babu ruwan su da ziyarar da Tinubu zai kai Ribas, ta ƙashin kan sa ce. Ya ce APC ta nesanta kan ta da ziyarar.
“Mu na ƙalubalantar gwamna mai barin gado Wike ya daina yi mana shisshigin tsarma mana siyasar raba kawuna. Domin babu abin da ya ke yi a Ribas sai raba kawunan ‘yan APC.
“Mu na sane yadda Wike ke ta nuna wa duniya cewa kamar APC ta mutu a Jihar Rivers, duk kuwa da ya sha furtawa a cikin hirarrakin da aka yi da shi a baya cewa, ba zai taɓa yin wata mu’amala da APC ba, domin jam’iyya ce mai ɗauke da cutar kansa.
Idan ba a manta ba, lokacin yaƙin neman zaɓe, sai da Tinubu ya kai wa Wike ziyara a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas.
A wurin ne har Wike ya shawarci Tinubu, ya ce masa kada ma ya yi asarar kuɗaɗen sa a zaɓen gwamna, domin ɗan takarar APC dai na jihar ba zai iya taɓuka komai ba.