Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), ta bayyana cewa a duk shekara sama da mutum 40,000 ke mutuwa wasu na samun nakasa dalilin haɗurran motoci a ƙasar nan.
Babban Jami’in FRSC, Dauda Biu ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja, yayin da ya ke jawabi a Makon Kula da Kiyaye Haɗurra ta ta 7 ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ya ce yawan waɗannan adadin mace-mace da nakasa duk haɗurran ababen hawa ne ke haddasa su a ƙasar nan.
Biu ya ƙara da cewa a duniya duk shekara haɗurra na salwantar da rayuka miliyan 1.3, sannan kuma fiye da mutum miliyan 50 na samun raunuka.
Ya ce haɗurra ne babbar barazana ga rayukan daga ‘yan shekara 5 zuwa 29. Ya ce mota da babura sun fi haddasa asarar rayukan jama’a.
“A Najeriya fiye da mutum 40,000 ke mutuwa sanadiyyar hatsari kan titi.” Inji Biu.
Ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi ƙudirin rage yawan haɗurra da kashi 50 bisa 100 nan da shekara ta 2030.
Idan ba a manta ba, Shugaban Cibiyar Kula da Kansa na Najeriya ya Bayyana cewa cutar kansa ta kashe mutum 78,000 cikin 2020 a Najeriya.
Hakan na nufin kenan a ƙiyasi, cutar kansa da haɗurra sun kashe mutum kimanin 120,000 cikin shekarar 2020.