Gwamna mai barin gado na Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari cewa kada ya rattaba hannun amincewa Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya tafi karatu ƙasar waje.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ga PREMIUM TIMES, Matawalle ya ce Emefiele ya na neman samun damar arcewa ya bar ƙasar ce kafin ƙarshen mulkin Buhari, “domin ya kauce wa titsiyewar da za a yi masa” dangane da bayani dalla-dalla kan abin da ya faru a CBN a ƙarƙashin mulkin Emefiele ɗin.
Gwamnan CBN ne mai sa-ido kan harkokin kuɗaɗe. Shi ne algungumin da ya kitsa tsarin sauya launin kuɗi da ƙwace wa mutane kuɗaɗen hannun. Wannan lamari kuwa ya haddasa matsanancin ƙuncin rayuwa a cikin Najeriya baki ɗaya.
“Amma kuma wai yanzu wannan Emefiele ɗin ne ke neman amincewa ya tafi hutun zuwa Turai karatu, alhali ya na da saura watanni 10 kafin ya cika wa’adin sa.
“Ƙarya ya ke yi, ya ƙirƙiri shirin tafiya karatu waje ne don kada gwamnati mai hawa ta titsiye shi yin bayanin gidogar da ya yi a CBN.”
Har yanzu dai ba a ji daga bakin Emefiele ko CBN ba cewa Gwamnan zai fice idan Buhari ya ba shi dama ba.
Miliyoyin mutane a faɗin ƙasar nan sun ɗora wa Emefiele laifin wahala da ƙuncin da aka shiga a farkon shekarar nan, saboda sauya launin kuɗi.
Wata gagarimar matsala baya ga canji kuɗi da Emefiele ya haifar wa ƙasar nan, ita ce yadda ya bai wa Gwamnatin Buhari kuɗaɗen CBN bashi har na naira tiriliyan 23.7, ba tare da sanin Majalisar Dattawa da ta Tarayya ba
Hakan ya haifar da Gwamnatin Buhari za ta sauka ta bar bashin naira tiriliyan 23.7 da karɓa ba bisa ƙa’ida ba a CBN.
A farkon watan Janairu ne wannan jaridar ta buga bayanin cewa zaune ta tashi tsaye a Majalisar Dattawan Najeriya, yayin da su ka gano cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bai wa Gwamnatin Buhari ramcen tsabar kuɗi har naira tiriliyan 23.8 a cikin shekaru bakwai, ba bisa ƙa’ida ba.
Yadda Aka Bankaɗo Rufa-rufar:
A ranar Laraba ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ƙoƙarin neman amincewar Majalisar Dattawa ta sa hannu cewa ta amince CBN ta bayar da bashin, wanda an rigaya an karɓa, har an dagargaje kuɗaɗen. Shi ne maimakon gwamnatin Buhari ta nemi amincewar Majalisar Dattawa, sai yanzu ta nema a makare, bayan an karɓa, an kashe tuni.
Na farko dai gwamnatin Buhari ki kuma a ce Shugaba Buhari ya karya doka, saboda ya yi ta karɓar kuɗaɗen daga CBN ba tare da neman amincewar Majalisar Dattawa ba.
Na biyu, CBN da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele sun karya doka, domin sun bai wa Gwamantin Buahri bashin da ya wuce ƙa’idar da ya kamata a bayar har sau 2900%.
Adadin Nawa Dokar Najeriya Ta Ce CBN Ya Ramta Wa Gwamnatin Tarayya?:
Dokar CBN ta cikin Kundin Dokokin Najeriya ta ce, “idan gwamnatin tarayya na fama da giɓin kasafin kuɗaɗe, za ta iya ramcen kuɗi daga CBN. Amma adadin da CBN zai bayar kada ya wuce kashi 5% kacal na jimlar kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayya ta samu a shekarar da ta gabata.”
Illar Wannan Bashin Rufa-rufa:
Wannan bashi a gwamnatin Buhari ta ci daga CBN ba bisa ƙa’ida ba, ya karya doka, ya haifar da tsadar rayuwa, ƙuncin rayuwa, hauhawar farashi, gurguncewar tattalin arziki da kuma jibga ɗimbin bashi a wuyan kowane ɗan Najeriya, har waɗanda za a haifa nan da shekaru masu zuwa.
Bashin Nawa Buhari Ya Gada Daga CBN:
Lokacin da Buhari ya hau mulki a Mayu, 2015, ya taras da bashin naira biliyan 789.7 da gwamnatin baya ta ciwo daga CBN.
Amma tsakanin Janairu zuwa Oktoba 2022, kaɗai a wannan shekarar, Gwamnatin Buhari ta ciwo bashin naira tiriliyan 5.6 daga CBN.
Tsakanin 2012 zuwa Mayu, 2015 kafin hawan Buhari, CBN na bin gwamnatin tarayya bashi na naira biliyan 654.9 kacal.