Ɓaraka ta haifar da saɓani tsakanin Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila da mataimakin sa, Idris Wase, inda ta kai su ga yin fito-na-fito a ranar Laraba.
Tsawon shekaru huɗu huɗu dai ba a taɓa samun wani saɓani tsakanin Gbajabiamila da Wase ba.
Sai dai kuma a yanzu su biyu ba su jituwa, saboda Wase wanda ya sake lashe zaɓen sa, ya fito ƙarara ya na neman takarar Kakakin Majalisar Tarayya.
Hakan kuwa na nufin Wase ya yi fatali da Tajuddeen Abbas wanda Tinubu da APC ke goyon baya kenan.
Gbajabiamila kuma bai sake fitowa takara a majalisa ba. A yanzu kusan za a iya cewa shi ne zai zama Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, idan an rantsar da Bola Tinubu.
Shi ma Gbajabiamila, ya na goyon bayan Tajuddeen Abbas ne, ba ya goyon bayan mataimakin sa Idris Wase.
Lamari ya dagule yayin rufe zaman Majalisa na ranar Laraba, yayin da Gbajabiamila ya umarci Shugaban Kwamitin Bin Ƙa’idoji Hassan Fulata, ya ce ya rubuta lokacin tashi daga Majalisa, saboda ya na so zai halarci wani taro.
Faɗin haka ke da wuya, sai Mataimakin sa Wase ya ce ya na da magana.
“Kakakin Majalisar Tarayya lamarin na ka ya zama abin dariya, kuma wasan yara ma kenan. Mun yi asarar lokuta masu muhimmanci. Don me za mu ture muhimman batutuwan da ke gaban majalisa saboda kawai ka na so ka halarci buge wasu ayyuka a wani wuri can daban? Don Allah ka yi watsi da zuwa buɗe ayyukan, mu ci gaba da abin da ya tara mu a nan kawai.
“Mu dai mu na nan. Duk mai son taɗiya wurin wani taro ya tashi ya tafi, amma dai kowa ya sani, babban abin da ke gabanmu shine aikin d mu ke yi wa ‘yan Najeriya waɗanda mu ke wa wakilci.”
Wannan batu ya sa su biyu ɗin su ka riƙa sa-toka-sa-katsi a tsakanin su.
“Wato kai Mataimaki na kamar ba ka san muhimmancin NILDS ba kenan, inda zan je buɗe ayyukan. Ai NILDS hukuma ce mai muhimmanci.” Inji Gbajabiamila.
A lokacin Wase tuni ya hasala ya miƙe tsaye, ya ce wa Gbajabiamila, “haba ya za ka ce ban san NILDS ba. Na sani mana.”
Daga su ka ci gaba da jayayya. Gbajabiamila na ƙoƙarin kare dalilin zuwa taron buɗe ayyuka, shi kuma Wase na ƙoƙarin nuna masa zaman majalisa ne abu mafi muhimmanci a gare su.
Ai kuwa sai Gbajabiamila ya fusata, ya ce: “Tun da ake dimokraɗiyya a Najeriya babu mataikakin da ya taɓa yin fito-na-fito da Kakakin Majalisa sai kai a yau. Saboda na daɗe a majalisa, amma ban taɓa ganin irin wannan yankan-ƙamna kamar abin da ka yi min yanzu ba.”