Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta kauce daga maimaita irin kurakuren da gwamnatocin Jonathan da Buhari su ka tafka wajen zaɓen shugabannin Majalisar Tarayya.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, inda ya tunatar da rikicin da ya haddasa Mambobin Majalisar Tarayya su ka zaɓi wanda ba shi jam’iyya ke so ba.
Ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya yi sakacin kasa iya riƙe ragamar mulkin sa tun a ranar Aminu Tambuwal ya zama Kakakin Majalisar Tarayya. Ya ƙara da cewa wannan lamari ne ya ƙara zama dalilin faɗuwar PDP a zaɓen 2015.
Shettima ya ce shi kuma Shugaba Mai Barin Gado, Muhammadu Buhari, ya kasa samun gagarimar nasara a shekaru huɗun sa na farko, saboda an zaɓi shugabannin majalisa waɗanda ba su ne jam’iyyar APC ke so ba.
Shettima ya bayyana haka yayin ganawar sa da Tajuddeen Abbas da Ben Kalu, waɗanda su ne APC da Tinubu ke so su zama Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.
An yi ganawar tare da gungu ko gamayyar mambobi masu biyayya ga zaɓin da jam’iyya ta bayar a batun shugabancin Majalisa.
Tuni dai mambobin da ba su goyon bayan Abbas da Ben Kalu, sun kafa ƙungiya, COPSA, wacce a ƙarƙashin ta su ke ta faɗa da Abbas da Ben Kalu da kuma uwar jam’iyya, APC.
Daga cikin masu adawa da Abbas, har da Mataimakin Kakakin Majalisa, Idris Wase, Shugaban Masu Rinjaye, Alhassan Doguwa, Sada Soli, Miriam Onuoha da Muktar Betara.
Dangane da wannan karankatakaliya, Shettima ya ce ya na magana da dukkan hasalallun ‘yan takarar, domin a cimma sasanta saɓanin.
“Zan yi ƙoƙari na ga na tuntuɓi dukkan sauran masu takara. Shi dai Honorabul Betara ɗan uwa na ne. Daga yanki ɗaya mu ka fito, kuma daga jiha ɗaya mu ka fito. Kuma akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin mu. Na gana da shi makonni biyu da su ka gabata. Zan kuma ci gaba da lallashin sa,” cewar Shettima.
Wajen ƙarfe 1 na yamma a yau kuma na gana da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya, Idris Wase. Za mu ci gaba da tuntuɓar juna.”
“Lokacin da Jonathan ya rasa ta-cewa a majalisa, ai kowa ya shaida yadda zangon sa na farko ya kasance bai yi abin kirki ba. Saboda ruɗanin da aka riƙa yi. Ba don komai ba saboda Jonathan ya yi sakaci Aminu Tambuwal ya zama Kakakin Majalisar Tarayya a lokacin.
“A yanzu ita ma Mariam Onouha akwai shaƙuwa tsakani na da ita. Zan tuntuɓe ta.”
Shugabancin Majalisar Dattawa: Dalilin Da Ya Sa Mu Ka Ce Sai Akpabio – Shettima
Shettima ya ce APC ta zaɓi Godswill Akpabio ne a matsayin wanda su ke so ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, saboda ba mu so a ce Shugaban Majalisar Dattawa ma Musulmi ne.
“Mu na so ne mu guje wa yadda za ta kasance shugaba Musulmi, Mataimaki Musulmi kuma Kakakin Majalisar Dattawa ma Musulmi. Kuma Kakakin Majalisar Tarayya shi ma Musulmi, duk addini ɗaya. Idan aka yi haka, za a yarda da masu cewa tabun ƙoƙarin maida Najeriya ƙasar Musulunci zalla gaskiya su ke faɗa kenan.
“Dalili kenan Tinubu ya yi hangen-nesan yin adalcin cewa tilas Shugaban Majalisar Dattawa ya kasance daga Kudu maso Kudu, kuma ya kasance Kirista ne, ba Musulmi ba.”
A na sa jawabin, Abbas ya yi wa Shettima alƙawarin cewa Majalisar Tarayya ta 10 za ta yi kyakkyawar dangantaka da mu’amalar aiki da ɓangaren gwamnati a cikin mutunci.
‘Ba Mu Amince Da Abbas Ya Zama Kakakin Majalisa Ba, ‘Lokaci Na Ne, A Ba Ni A Wuce Wurin’ – Wase:
Wase ya ce wannan ne lokacin da zai zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya, Idris Wase, ya fito ƙiri-ƙiri ya yi fatali da matsayar da APC da Tinubu su ka ɗauka, inda su ka bada shugabancin Kakakin Majalisar Tarayya ga Tajuddeen Abbas na Jihar Kaduna.
Wase, wanda a yanzu shi ne Mataimakin Femi Gbajabiamila tsawon shekaru huɗu, ya bayyana cewa shi ma yanzu lokacin da ne da zai zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Ya bayyana haka ranar Juma’a, a otal ɗin Transcorp Hilton, Abuja, inda a jawabin sa, ya ce shi ma ya ari salon da Bola Tinubu ya yi, na ‘Emi lokon’, ya ce “Ni ma yanzu ne lokaci na.”
“A wannan lokacin, zan ari salon karin maganar da oga na Bola Tinubu ya yi amfani da ita, ’emi lokan, emi lokan, emi lokan,” ya maimaita sau uku, watau “yanzu lokaci ɗaya ne.”
Wase wanda ya fito daga jihar Filato, ya ce tilas jam’iyya mai mulki ta bi tsarin da dokokin tsarin mulkin Najeriya ya shimfiɗa, ta yadda za su tabbatar da cewa ba a maida yankin su na Arewa ta Tsakiya saniyar-ware ba.
“Ya kamata a lura da cewa yankin Arewa ta Tsakiya ne kaɗai bai taɓa samar da Kakakin Majalisar Tarayya a Najeriya ba, tun daga komawar dimokraɗiyya cikin 1999 har zuwa 2023.