Sanatocin da za su kammala wa’adin su da zaɓaɓɓun da za su hau da ke Kudu maso Gabas, sun bayyana cewa ba su yarda ba, kuma ba za su amince da Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ba.
Sun jajirce cewa buƙatar su ita ce shugaban majalisar dattawa ya fito daga yankin Kudu maso Gabas, ba Kudu maso Kudu inda Akpabio ya fito ba.
Sun bayyana wannan matsayar da su ka cimma a ranar Lahadi, bayan sun tashi daga wani taron gaggawa a Abuja.
Idan ba a manta ba, Gwamna mai barin gado na Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa Gwamnonin APC sun yanke shawarar cewa Godswill Akpabio zai zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Hakan ya sa Sanata David Umahi daga Ebonyi ya janye takarar shugabancin majalisa da aka ce Tinubu ya roƙe shi ya janye.
Sauran ‘yan takara daga Kudu maso Gabas sun haɗa da Orji Kalu, Osita Izunaso da Patrick Ndubeze.
‘Duk Wanda Ya Yi Wa Akpabio Mubaya’a Ya Zaɓi Ci Gaban Maida Kudu-maso-gabas Saniyar-ware’:
Sanatoci 11 daga Kudu maso Gabas da su ka saka hannu kan yarjejeniyar cimma matsayar rashin goyon bayan Akpabio, sun ce amincewa da Akpabio tamkar ci gaba ne da mayar da Kudu maso Gabas saniyar-ware a mulkin Najeriya.
Daga nan sun yi kira ga Tinubu ya janye goyon bayan da ya bayar ga Akpabio, kuma ya daina nuna siyasar wariyar wani yanki.
Sun ce daga Kudu maso Gabas ya kamata a ce Tinubu ya fidda ɗan takarar da zai goya wa bayan zama shugaban majalisar dattawa.
Daga ɓangaren Arewa ma ana ƙalubalantar Akpabio, inda wata ƙungiya ta yi zargin cewa Akpabio ba ya ƙaunar ‘yan Arewa da yankin Arewa ɗin ɗungurugum.
Ƙungiyar ta ce, “Akpabio ba ya ƙaunar ‘yan Arewa, ba mu yarda ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ba”, cewar Sa’idu, Shugaban Dattawan Arewa Mazauna Kudu.
Kungiyar Dattawan Arewacin (ACF) ta nesanta kan ta daga wani gungun mutanen da su ka ce wai sun goyi bayan tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Shugaban ACF na kudancin ƙasar nan ne ya bayyana cewa ACF ba ta cikin wata ƙungiyar da ta kira kan ta ‘Coalition ot Northern groups, wadda ta ce ta goyi bayan Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa.
Sa’idu ya yi wannan sanarwa ce a ranar Lahadi, a Abuja.
Ya ce shugabancin Akpabio ya Majalisar Dattawa zai zama wani bala’i ga Arewacin Najeriya.
“Mu na sanar da cewa ba mu cikin waɗanda ke goyon bayan Sanata Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa. Kuma babu ruwan mu da gungun masu kiran kan su ‘Coalition of Northern Group’, waɗanda su ka ce sun goyi bayan Akpabio
“Waɗannan gungun mutane dai ba da yawun Arewa su ka yi katoɓarar goyon bayan Akpabio ba.
“Babu cikakken ɗan Arewa mai kishin Arewa da zai goyi bayan Akpabio, saboda ba ya ƙaunar Arewa.
“Mu ne mu ka san Akpabio, kuma mu ka san ko shi wane ne. Saboda mu ne ke zaune a Kudu, mu mu ka san ‘yan Kudu masu kaunar Arewa. Kuma maganar gaskiya Akpabio ba ya cikin masu ƙaunar Arewa.”
Sa’idu ya ce ko dai waɗanda su ka ce sun goyi bayan Akpabio sun yi ne a bisa rashin sani, ko kuma kuɗi aka ba su kawai.