A ranar Lahadi ce gungun wasu hasalallu su ka bayyana rashin amincewa da tsarin fitar da shugabannin Majalisar Tarayya, wanda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da APC su ka amince a bi domin fito da shugabannin.
A kan haka ne su ka yi kira cewa a a sake sabon lale.
Shi dai Tinubu an ce ya goyi bayan zaɓen Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa, sannan Sanata Barau Jibrin daga Arewa maso Yamma mataimakin sa.
An kuma ce ya amince Tajuddeen Abbas daga Kaduna ya zama Shugaban Majalisar Tarayya, shi kuma Ben Kalu daga Kudu maso Gabas mataimakin sa.
Wannan tsarin dai ya bar yankin Arewa ta Tsakiya ya tashi a tutar babu, duk kuwa da cewa mutum uku daga yankin da su ka haɗa da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya, Idris Wase, Yusuf Gagdi su biyu daga Filato da Olatunji Raheem daga Kwara, sun nuna son muƙaman.
Har yanzu dai Tinubu bai fito ya ce ga waɗanda ya ke goyon baya ba.
Gungun wata ƙungiyar tsoffin ‘yan majalisa sun ƙi amincewa da tsarin. Sun dai fito ne daga Arewa ta Tsakiya.
Sun ce tsarin da aka fito da shi ya maida Arewa ta Tsakiya saniyar-ware.
Su masu goyon bayan Mataimakin Kakakin Majalisa a yanzu, Idris Wase, sun ce ba su amince da tsarin ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta ruwaito cewa Tinubu ya ‘yarda’ Tajuddeen Abbas ya zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Alamomi masu ƙarfi kuma tabbatattu na nuna cewa Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya amince Honorabul Tajuddeen Abbas daga Jihar Kaduna ya zama Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, wato Majalisar Tarayya.
Haka kan kuma ya amince Ben Kalu daga Abia ya zama Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.
Idan hakan ta tabbata, to yankin Arewa ta Tsakiya ya tashi a cikin ‘yan-kalar-dangi kenan, ta yadda dukkan muƙamai shida ba su samu ko ɗaya ba.
Discussion about this post