Yayin da ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomin Zamfara ke bikin tunawa da zagayowar Ranar Ma’aikata a 1 Ga Mayu, har yau ba a biya su albashin watanni uku ba, yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da fatattakar mazauna karkakar yankunan faɗin jihar.
PREMIUM TIMES ta zanta da ma’aikata 15 na Jihar Zamfara, waɗanda su ka shaida wa wakilin mu cewa watanni uku kenan ba a biya su albashi ba.
Ma’aikatan dai sun nemi a sakaya sunayen su, saboda tsoron kada gwamnati ta bi su da bi-ta-ƙulli, sun ce wannan ne karon farko da su ka yi azumi da Ƙaramar Sallah babu albashi.
Yayin da mafi yawan ma’aikata ba a biya su albashi tun watan Fabrairu ba, kaɗan daga cikin ma cewa su ka yi su ko na watan Disamba ma ba a biya su ba.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Jihar Zamfara ta ce ta na faɗi-tashi ba dare ba rana, domin ganin an biya dukkan ma’aikatan haƙƙoƙin su.
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na Jihar Zamfara, Sani Halliru, ya shaida wa wakilin mu ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, “idan aka haɗa da albashin watan Afrilu da ba a biya ba, to ma’aikatan Zamfara na bin albashin watanni uku kenan ba a biya su ba.”
“Abin da yanzu ake ciki a Zamfara shi ne, mu na da ma’aikatan da ba a biya su albashin wata biyu ba. Waɗannan sun fi yawa, kuma akwai ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi a cikin su. Waɗanda aka biya cikin Fabrairu ba su taka kara sun karya ba.” Inji Shugaban NLC na Zamfara.