Jigon PDP Ladi Adebutu, wanda a makon jiya ya tsere daga Najeriya, sannan daga waje ya ce ya gudu ne saboda wasu na neman halaka shi, yanzu ya shiga tsomomuwa bayan ‘yan Sandan Najeriya sun ce ya gudu ne saboda sun bankaɗo wata gadangarƙamar da ya shirya, ta sayen ƙuri’u da naira biliyan 2 a lokacin zaɓen 2023.
‘Yan sanda sun ce Adebutu wanda ya yi takarar gwamnan Ogun a ƙarƙashin PDP, ya yi watandar naira biliyan 2 a faɗin jihar, domin a sayi ƙiri’un masu zaɓe a zaɓen gwamna na ranar 18 Ga Maris.
Wannan zargin da ake yi masa, ya na cikin rahoton da ‘yan sandan bincike su ka gabatar wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.
Shugaban APC na Jihar Ogun, Abdullahi Sanusi ne ya aika wa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun takardar ƙorafi, su kuma su ka gudanar da bincike.
Yadda Adebutu Ya Shiga Tsomomuwa:
Abdullahi Sanusi ya rubuta wasiƙar ƙorafin ce zuga ga ‘yan sanda, a ranar 18 Ga Maris, wato ranar zaɓe. Ya yi adireshin wasiƙar ga Sufeto Janar na Ƙasa.
A cikin takardar ƙoƙarin, ya ce Adebutu ya riƙa raba katin ATM wanda kowane an loda masa Naira 10,000 a cikin asusun. An riƙa raba su a ranar zaɓe.
Daga nan aka naɗa ‘yan sandan bincike a ƙarƙashin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Mohammed Babakura, da ke Ofishin Binciken Manyan Laifuka (CID), a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Adebutu ya samu ƙuri’u 262,383, ya zo na biyu, shi kuma Gwamna Dapo Abiodun na APC, ya sake lashe zaɓe a karo na biyu kenan, da ƙuri’u 276,298.
Rashin nasarar da Adebutu ya yi da bambancin ƙuri’u 14,000 kacal, sai ya garzaya kotun sauraren ƙararrakin zaɓe, ya maka Gwamna Abiodun ƙara a kotu.
A ranar 14 Ga Mayu, PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Adebutu ya ce ya tsere daga Najeriya ce, saboda wasu da bai bayyana ko su wa ne ba na neman halaka shi.
To sai dai kuma rahoton bayan binciken da ‘yan sandan bincike ƙarƙashin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Mohammed Babakura su ka bayar, sun ce lokacin da su ka gayyace shi, ya tura lauyoyin sa, su ka shaida wa masu bincike cewa Adebutu ya fita ƙasar waje ganin likita.
Wannan jarida ta kira lambar wayar Adebutu a ranar Lahadi, amma bai ɗauka ba.
Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labaran sa Afolabi Orekoya ya ƙaryata zarge-zargen da ake yi masa.
Shugaban APC na Ogun, Abdullahi Sanusi, ya rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda takardar ƙoƙarin cewa Adebutu ya riƙa amfani da katin ATM, samfurin ‘Verve’, wanda aka buga masa na musamman, mai ɗauke ɗauke da sunan mahaifiyar sa ‘Dame Caroline Oladunni Adebutu Endowment Scheme’, kowane ɗaya an loda masa kuɗi Naira 10,000 a ciki.
An riƙa raba katin ATM ɗin a rumfunan zaɓe, a ranar zaɓe.
“Kuma PDP ta girke matasa masu P.O.S birjik a kowace rumfar zaɓe, inda duk wanda aka damƙa wa ATM kyauta, sai kawai ya je wurin mai P.O.S ya cire kuɗin sa hankali kwance.”
‘Yan sanda sun ce yayin da su ka samu wannan ƙorafin, sai jami’an su tare da jami’an NDLEA su ka kama mutum biyar ɗauke da irin katin ATM ɗin da ake magana, a ranar zaɓen.
“An samu katin ATM har guda 131 a hannun wata mata mai suna Adejoke Sanni, sai kuma sauran mutum huɗu da aka same su da katin ATM 52. Dukkan su kuma ‘yan jam’iyyar PDP ne.”
‘Yan sanda sun kuma kama wasu masu P.O.S ɗin da aka riƙa cirar kuɗaɗen a hannun su. Daga nan kuma aka gano cewa karin ATM ne na musamman, na Bankin Zenith ne.
‘Yan sanda sun tuntuɓi Zenith Bank da Hukumar CAC, inda Zenith ya shaida masu cewa Adebutu kwastoman bankin ne tun cikin 2009.
Ya tuntuɓi bankin a cikin Fabrairu, ya ce ya na so a yi masa katin ATM na musamman, domin ya yi amfani da shi ya raba tallafin kuɗaɗe ga marasa galihu, a ranar tunawa ko zagayowar ranar rasuwar mahaifiyar sa.”
Babban Jami’in Zenith Bank Clestine Appeal ya shaida wa ‘yan sanda cewa Adebutu ya nemi a yi masa katin ATM guda 200,000, kowane a loda masa naira 10,000, kuma hakan aka yi masa. An loda Naira biliyan 2 kenan a cikin su.
Rahoton ‘yan sanda ya nuna Adebutu ya karɓi dukkan katin a ranar 27 Ga Fabrairu, kuma an loda wa dukkan katin kuɗi a ranakun 16 da 17 Ga Maris, 2023, kwanaki biyu da kafin ranar zaɓen gwamna, da kuma ranar jajibirin zaɓen gwamna.
Daga nan ‘yan sanda sun gayyaci Adebutu, ba sau ɗaya ba, maimakon ya je, sai ya arce ya bar ƙasar.