Kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya fara mulkin sa da karakainar yawan zuwa Ingila kula da lafiyar sa, a yanzu ɗin ma ya ƙare mulkin na sa da tafiya Landan neman maganin ciwon haƙori.
Yayin da saura makonni uku Shugaba Buhari ya miƙa mulki bayan cikar wa’adin sa na tsawon shekaru takwas, a yanzu Buhari ya na Landan tun ranar 3 Ga Mayu, inda bayan ya halarci bukin miƙa Sandar Mulki ga Sarkin Ingila Charles lll a ranar 6 Ga Mayu, sai Buhari ya ƙara zaman sa na tsawon mako ɗaya, domin litikocin sa su ƙara duba shi.
Sanarwar dalilin tsayawar da Buhari ya yi a Landan ta fito ne daga bakin Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Femi Adesina, a ranar Talatar da ta gabata.
Wannan batun tsayawa neman magani da ya yi, ta fusata mutane da dama, har su ka riƙa tuna yadda tun bayan watanni takwas da hawan sa mulki ya fara tafiya ganin likita, har abin da ya kai shi ya na zuwa jiyya. Gaba ɗaya a zamanin mulkin sa ya shafe kwanaki 225 a Landan zaman jiyya da ganin likitoci. Lissafin nan ya tsaya ne zuwa ranar 4 Ga Disamba, 2022.
Ya kamata Buhari ya sani cewa ciwon hakori fa abu ne da za a iya magance maka shi a nan Najeriya. Maƙudan kuɗaɗen da aka narkas kan haƙorin ka da kuma tulin kuɗaɗen da aka caje ka saboda jirgin saman ka na ajiye a filin jirgin Landan bisa caji mai tsada, saboda ƙarin kwanakin da ka ƙasa, har tsawon sati ɗaya.
Zirga-zirgar Buhari Landan Ganin Likita:
Buhari ya fara tafiya neman magani zuwa Landan a ranar 5 Ga Fabrairu, 2016 inda ya shafe kwanaki 6.
Sai kuma ranar 23 Ga Janairu, 2017, ya tafi jiyyar kwanaki 50, wadda sai a ranar 10 Ga Maris ya dawo Najeriya.
Tafiya Landan jiyya mafi daɗewa da Buhari ya yi, ita ce wadda ya shafe kwanaki 104, kuma har yau ba a bayyana rashin lafiyar da ta kwantar da shi har kwanaki 104 ɗin ba.
Dukkan waɗannan kwanaki za a ga cewa Buhari ya zarce marigayi Umaru ‘Yar’Adua daɗewa jiyya ko tafiya waje neman magani. Domin shi Umaru kwanaki 172 ya shafe a waje, shi kuma Buhari sama da kwanaki 230, idan aka haɗa har da wannan tafiya ta baya-bayan nan da aka ce ya tsaya neman maganin ciwon haƙori.
Abin baƙin ciki ne a ce har yau ɗin nan an kasa ko an ƙi bayyana wa ‘yan Najeriya adadin maƙudan kuɗaɗen da aka kashe tsawon shekaru takwas ana neman maganin matsalolin da ke damun Buhari.
Amma dai abin da aka sani ne cewa a cikin shekaru takwas Buhari ya ziyarci sama da ƙasashe 40, an kashe naira biliyan 50.75 wajen kula da jiragen Shugaban Ƙasa daga 2015 zuwa Disamba, 2022.
Wata jarida ta ce idan har za a kashe waɗannan kuɗaɗe kan jirgin Shugaban Ƙasa, haka kuɗaɗen da aka kashe kan neman lafiyar shugaban ƙasa ɗin masu yawa ne matuƙa.
Har yau tun da Buhari ya hau mulki har zai sauka, ba a taɓa duba lafiyar sa a asibitin cikin Najeriya ba, na gwamnati ko na masu zaman kan su. Duk tsanani ko ƙanƙantar ciwo, Buhari Landan ya ke tafiya. Hakan ya bai wa gwamnoni damar yawan ficewa fita neman maganin har ƙanana cututtuka a waje.
Abin takaici ne duk da maƙudan kuɗaɗen da ake ware wa Asibitin Fadar Shugaban Ƙasa, wanda aka gina don kula da lafiyar sa da iyalan sa, a ce ya kasa kula da shugaban.
A cikin 2022 an kashe wa asibitin naira biliyan 20.8. Cikin 2017 sai da A’isha Buhari da Zahra Buhari su ka ragargaji yadda ba a kulawa da asibitin na cikin Fadar Shugaban Ƙasa.
Gwamnatin Buhari ta sha fama da matsalolin likitoci da yawan yajin aiki, neman haƙƙin ma’aikatan lafiya da kuma gudun da likitocin ƙasar nan ke yi zuwa ƙasashen Turai, Saudiyya da wasu ƙasashe.
A yanzu haka a Ingila, ƙasar da Buhari ke zuwa ganin likita, akwai likitocin Najeriya a can za su kai 10,296.
Ingila da Indiya su na samun dala biliyan 2 daga Najeriya duk shekara, sanadiyyar masu zuwa ƙasashen ganin likita. Shekaru biyu da su ka gabata ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana haka.
Duk shugaban da bai yarda da asibitocin cikin ƙasar sa su riƙa duba shi ba, sai dai su duba talakawan sa, haƙiƙa bai ɗauki lafiyar talakawan sa da muhimmanci ba.
Ta Buhari dai ta zo ƙarshe. Saura kuma mu ga kamun ludayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado. Bisa dukkan alamu kuma ba canja zani za ta yi ba.
Discussion about this post