A yanzu dai ƙaryar kwaram-kwaram ta ƙare, tunda mai kalangu ya faɗa ruwa. A yau ne wa’adin shekaru takwas na mulkin Buhari ya ƙare, yayin da magajin kujerar mulkin sa Bola Tinubu zai karɓi ragamar mulki a hannun sa. A cikin ƙasa kuma ana ta gardandamin shin gyara Buhari ya yi, ko kuwa gyaran gangar Abzinawa ya yi?
Buhari ya sadaukar da makonnin na ƙarshe biyu ya na buɗe ayyukan da wasu a cikin su ana ta yi masa sam-barka har ma daga ɓangaren waɗanda su ka fi kowa sukar sa.
Shi kan sa gogan, ya yi amanna cewa zai sauka daga mulki zai bar ƙasar nan fiye da lokacin da ya same ta a 2015. Sai dai kuma abin da ya ke ta nanatawa ɗin, babu shi a aikace. Saboda gaskiyar magana ayyukan da Buhari ya yi ba su kai a jinjina masa ba, idan aka yi la’akari da dalilan da su ka sa aka zaɓe shi tare da tunanin da kowa ya yi kan abubuwan da ake tunanin idan ya hau zai magance.
A lokacin mulkin Buhari ƙwaƙwalwar talakawa ta shekara takwas ta na zaɓaɓɓaka, saboda gyarar da riƙa gasa masu a ka. Buhari ya kafa tahirin take dokar ƙasa da yin fatali da ƙa’idojin da tsarin mulki ya tanadar. Sannan sau da dama wasu matakan da ya ke ɗauka tsari ne kawai na ‘yan gidoga.
Buhari ya hau mulki albarkacin gazawar da wanda ya karɓi mulkin a hannun sa ya yi. Yau hau mulki ɗauke da alƙawurran magance cin hanci da rashawa, magance matsalar tsaro da kuma farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya. Sai dai kuma kaico. Tun tafiya ba ta yi nisa ba sai ‘yan Najeriya su ka sadaƙas, su ka dawo daga rakiyar sa, ganin yadda fito ƙiri-ƙiri a naɗe-naɗen muƙamai ya yi watsi da cancanta, ya bada fifiko wajen naɗa daya daga makusantan sa, sai fifita ‘yan yankin sa, sai nuna ƙabilanci da ɓangaranci. Kenan, kalaman sa da ya yi a ranar da aka rantsar da shi, inda ya ce “ni na kowa ne”, sun zama tatsuniyar Gizo da Ƙoƙi kenan.
Wannan ko shakka babu, matsalar tsaro ce babban ƙalubalen da Buhari ya gada. A lokacin Arewa, musamman Arewa ta Gabas da ta ƙunshi jihohin Barno, Yobe da Adamawa, kai har ma FCT Abuja ita kan ta, sun rincaɓe da tashin bama-bamai da kashe-kashe. Zuwan Buhari ya kawo wa mazauna yankunan tunanin samun sauƙi. Musamman da ya ce, ba za a taɓa cewa an daƙile Boko Haram ba, har sai ranar da aka ceto dukkan ɗaliban Chibok da Boko Haram su ka yi garkuwa da su.
To me ya faru daga nan? Har yau ranar da Buhari ya sauka daga mulki, fiye da kashi 90 bisa 100 na ‘yan matan Chibok na hannun Boko Haram. Babban abin takaici kuma dubban ‘yan Najeriya sun ci gaba da ɗanɗana irin halin da ɗaliban Chibok su ka tsinci kan su a ciki.
Duk da haka, za a iya cewa an samu nasarar kakkaɓe Boko Haram masu yawan gaske, tare da hana su yin dogon zangon kai hare-hare. Kuma zaman lafiya a hankali na samuwa a yankin Arewa maso Gabas.
Sai dai fa a yau ɗin nan, Najeriya ba ta taɓa samun kan ta cikin matsalar tsaro ba, kamar yadda ta tsinci kan ta a zamanin mulkin Buhari. Kashe-kashen Fulani makiyaya da ‘yan bindiga da sauran gungun masu aikata manyan laifukan kisa da garkuwa, musamman a Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Gabas, sun maida Najeriya ƙasar da rayukan bil Adama ba shi da wata daraja.
Buhari ya sauka ya bar tsarin ‘yan sanda maras kayan aiki, rashin isassun ‘yan sanda, waɗanda ake da su ɗin sun tattare cikin birane, yawanci a jikin masu mulki, an bar gaba ɗayan yankunan karkara a hannun ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, masu kai hare-haren tarwatsa ƙauyuka daban-daban.
An kashe áƙalla mutum 53,418 waɗanda kafafen yaɗa labarai su ka bayyana kisan su. Kamar yadda lissafin ƙididdigar da ‘Nigerian Security Tracker’ ya bayyana, cewa an kashe wannan adadi daga ranar da aka rantsar da Buhari, 29 ga Mayu, 2015 zuwa 15 Ga Oktoba, 2022.
Ba fa a yaƙin ƙarilan-maƙatulan na fito-na-fito aka yi wannan kisan ba, kisa ne na hare-hare da tashe-tashen hankula a yankuna daban-daban.
Mummunan kashe-kashen kwanan nan da aka yi a Benuwai da Filato da Zangon Kataf a Jihar Kaduna, sun sake nuna cewa Buhari dai ba dattijon da ke tausayin talakawa ba ne, kuma ba shi da kwarjinin da zai iya kusantuwa da su a duk lokacin da wani Ibtila’i ya ritsa da su.
Kashe-kashen ƙabilanci da hare-haren ‘yan bindiga sun maida dubban ƙananan yara marayu, dubban mata sun zama zawarawa, har mazauna sansanin masu gudun hijira sun kai miliyan 3.2 a ƙididdigar cikin watan Afrilu, 2022 da Wakilin Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHRC), Chansa Kapaya ya bayyana.
Har yau ranar da Buhari ya sauka, ba a sake jin yadda aka yi da ‘yan canji 400 da aka kama bisa zargin ɗaukar nauyin Boko Haram ba. Kada a manta, an kama su tun cikin watan Maris, 2022.
Sai dai fa kada a manta, Gwamnatin Buhari ta taɓuka wajen tabbatar da wasu nasarori. Ba don goyon bayan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya riƙa bai wa Aliko Ɗangote ba, da matatar ɗanyen man da aka gina wadda za ta riƙa tace ganga 650,000 a kullum ba ta yiwu ba.
Buhari ya gina titi tsawon kilomita 8,852.94 daga 2016 zuwa 2022. Kamar yadda tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola ya bayyana.
Buhari ya gyara manyan titina 12 masu tsawon kilomita 896. Daga ciki akwai titin Lagos zuwa Ibadan, Enugu zuwa Fatakwal, Kaduna zuwa Kano. Ga kuma doguwar gasar Kogin Neja, ga titin jirgin ƙasa na Legas zuwa Ibadan mai nisan kilomita 156, na Abuja zuwa Kaduna, Itakpe zuwa Warri da sauran wasu ayyuka.
Sai dai kash, ‘yan bindiga sun mamaye wasu yankunan, sun hana matafiya cin moroyar waɗannan tituna da aka gina ko aka gyara. Haba jama’a. Sai da aka biya Naira miliyan 800 sannan ‘yan bindiga ko ‘yan ta’adda su ka saki mutum bakwai daga cikin fasinjojin da su ka yi garkuwa da su cikin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna. Wani ɗan ƙasar waje a cikin su kuwa shi miliyan 200 ya biya sannan aka sake shi.
Ƙoƙarin da Buhari ke ganin ya yi a ɓangaren tattalin arzikin ƙasa da noma, bai yi tasiri ba, domin maƙudan kuɗaɗen da aka kashe wajen bunƙasa noma a cikin ƙasa bai zama alheri ga talakawa ba, sai ma tsadar rayuwa da aka ƙara jefa miliyoyin mutane. Farashin kayan abinci a nunka ya ƙara ruɓanyawa, fiye da lokacin da ake sayen su kafin a rufe kan iyakoki ko hana shigo da wasu kayan abinci daga ƙasashen waje.
Tsadar rayuwa ta yi katutu. Mabarata ne ko ina cikin garuruwa da biranen ƙasar nan. Kan titi da cikin kasuwanni kuwa mutane na roƙon abin da za su ci, ko kuɗin mota. Rashin aikin yi ya yi muni sosai.
Buhari ya hau mulki buhun shinkafa ya na naira 5,587 a wasu yankunan Najeriya a 2015. Buhari ya sauka buhun shinkafa ya na naira 30,000, wani ma har 50,000.
Yankuna da dama a Arewa, ciki har da jihar da Buhari ya fito, Katsina, kashe-kashen ‘yan bindiga da garkuwa sun hana manoma zuwa gona.
A ƙarƙashin mulkin Buhari, Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ta ce Malejin Tantagaryar Talauci da Fatara ya tabbatar akwai mutum miliyan 133 da ke fama da gaganiyar neman cin yau ko na gobe, ko su samu ko ba su samu ba. Su na kwana da tashi cikin talauci da fatara.
Buhari ya hau mulki Dalar Amurka ba Naira 220 a kasuwar ‘yan canji. Ya sauka ya bar ta a Naira 750.
Tarihi ba zai taɓa manta cewa an yi Shugaba Muhammadu Buhari ba, mutumin da ya ciwo wa ƙasar nan bashin Naira tiriliyan 77. Kusan fiye da kashi 90 na kuɗaɗen shigar da ake samu a ƙasar nan, su na tafiya ne a biyan basussuka. Alhali ya hau mulki ya samu abin da ake bin Najeriya bashi bai wuce Naira tiriliyan 12.12 ba.
Haka kuma ba za a manta da yadda ya riƙa tsine wa tallafin man fetur kafin ya hau mulki ba. Bayan ya hau kuma ya fi kowane shugaba biyan tallafin fetur Naira biliyan 400 duk wata.
A gaban Buhari, tunda shi ne Ministan Fetur tsawon shekaru takwas na mulkin sa, an saci ɗanyen mai na dala biliyan 3.2, tsakanin Janairu 2021 zuwa Fabrairu 2022, cikin shekara ɗaya. Cikin Oktoba 2022 an gano ƙananan matatun mai har 58 da ake tace man sata a zamanin mulkin Buhari, kuma shi ne Ministan Fetur.
Idan aka koma batun yaƙi da cin hanci da rashawa, har yau abin ya na ɗaure kai a ce Buhari ya kasa ƙwato dala biliyan 17 na kuɗaɗen fetur ɗin da aka sace tsakanin 2011 zuwa 2014.
Buhari ya saki ɓarayin gwamnati waɗanda aka ɗaure a kurkuku. Akwai wasu shari’un tsoffin gwamnoni 11 da aka yi walle-walle da su, bayan EFCC ta gurfanar da su.
Zuwa Afrilu 2022, ma’aikatun gwamnatin tarayya sun kasa maida Naira tiriliyan 5.2 da ba su kashe daga kasafin kuɗaɗen su ba. Har yau daga cikin waɗannan tiriliyan 5.2, naira biliyan 53 5 kaɗai aka ƙwato cikin watanni 18, kamar yadda tsohuwar Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ta tabbatar.
Buhari zai sauka ya bar yara miliyan 20 masu gararamba kan titi, ba su zuwa makaranta. Alhali ya gaji yara miliyan 13.2 ba su zuwa makaranta a zamanin mulkin Jonathan.
Kada a manta, a zamanin mulkin Buhari ne aka samu manyan jami’an sa na sata ta fitar hankali. Ku dubi dai satar ɗanyen mai alhali shi ne Ministan Fetur. To kada ku manta an yi Akanta Janar da ya kantara satar naira biliyan 84 a ƙarƙashin mulkin Buhari.
Shin wane ‘ceto’ Buhari ya yi, a shekaru takwas ya na mulki. Ina gaskiyar da ake masa kirari da ita, kafin ya hau mulki da ake ta cewa, ‘Najeriya sai mai gaskiya’!
Discussion about this post