Shugaban Hukumar Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), Yisha’u Ahmed, ya jaddada cewa katin shaidar aikin yi wa ƙasa hidima da Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah ya mallaka, na jabu ne.
Wannan iƙirarin da ya yi ya fusata jam’iyyar PDP, wadda zaɓaɓɓen gwamnan ya yi nasara a ƙarƙashin ta.
Mbah, ɗan PDP kuma wanda ya lashe zaɓen gwamna a ranar 18 Ga Maris, ya ƙaryata zargin da NYSC ke yi masa, ba sau ɗaya ko sau biyu ba.
Ya haƙiƙice cewa ya kammala aikin bautar ƙasa a Jihar Legas, kuma bayan kammalawa sai Hukumar NYSC ta damƙa masa satifiket.
Hukumar dai ta na bayar da shaidar ce ga wanda bai wuce shekaru 30 da haihuwa ba, bayan ya kammala bautar ƙasa ta shekara ɗaya.
PDP ta hasala saboda Shugaban NYSC ya shaida cewa katin shaidar bautar ƙasa na Zaɓaɓɓen Gwamnan Enugu, na bogi ne.
Shugaban Hukumar Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), Yisha’u Ahmed, ya jaddada cewa katin shaidar aikin yi wa ƙasa hidima da Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah ya mallaka, na jabu ne.
Wannan iƙirarin da ya yi ya fusata jam’iyyar PDP, wadda zaɓaɓɓen gwamnan ya yi nasara a ƙarƙashin ta.
Mbah, ɗan PDP kuma wanda ya lashe zaɓen gwamna a ranar 18 Ga Maris, ya ƙaryata zargin da NYSC ke yi masa, ba sau ɗaya ko sau biyu ba.
Ya haƙiƙice cewa ya kammala aikin bautar ƙasa a Jihar Legas, kuma bayan kammalawa sai Hukumar NYSC ta damƙa masa satifiket.
Hukumar dai ta na bayar da shaidar ce ga wanda bai wuce shekaru 30 da haihuwar ba, bayan ya kammala bautar ƙasa ta shekara ɗaya.
Cikin watan Fabrairu ne NYSC ta fitar da sanarwa ta hannun Daraktan Bada Katin Shaida, Ibrahim Muhammad cewa, Satifiket ɗin da Mbah ya mallaka ba daga hukumar ta NYSC ya same shi ba.
Daga nan sai Mbah ya garzaya kotu, inda ta bayar da umarnin cewa kada NYSC ta ƙara cewa ba daga hukumar satifiket ɗin ya fito ba.
Daga nan kuma sai zaɓaɓɓen gwamnan ya maka NYSC kotu, har ya nemi ta biya shi diyyar naira biliyan 20, diyyar ɓata masa suna da hukumar ta yi. Ya shigar da ƙasar a Babbar Kotun Tarayya a Abuja.
Za dai a rantsar da Mbah a matsayin Gwamnan Enugu a ranar 29 Ga Mayu, 2023.
A tattaunawar da aka yi da Shugaban NYSC, Ahmed a Gidan Talbijin na Arise TV, ya ƙara jaddada cewa katin shaidar NYSC na zaɓaɓɓen gwamnan, na bogi ne.
Sai dai kuma PDP reshen jihar Enugu ta bakin kakakin kamfen ɗin ta, Nana Ogbodo, ya ce Shugaban NYSC ɗan tuggu ne kuma maƙaryaci, mayaudari.
Discussion about this post