‘Yan-gaban-goshin sanatocin da APC ke so su zama Shugaba da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Sanata Barau Jibrin, sun kai ziyara ga Gwamnan Jihar Katsina mai barin gado, Aminu Masari.
Sanatocin biyu su na kai masa ziyarar ce tare da masu take masu baya, waɗanda su ka haɗa da Sanata Solomon Oamilekan na Legas, Opeyemi Bamidele na Ekiti, Yusuf Yusuf na Taraba.
A yayin ziyarar wadda su ka kai masa a ranar Lahadi, sun nemi goyon bayan Gwamna Masari wajen ganin buƙatar APC ta Akpabio da Jibrin su zama shugabannin Majalisar Dattawa ta tabbata.
Yayin da wasu sanatoci da dama su ka ƙi amincewa da Akpabio da Barau Jibrin, shi kuwa Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana dalilan da su ka sa Tinubu ya jajirce cewa sai Akpabio ne zai zama shugaban majalisar dattawa.
Kashin Shettima, Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya bayyana dalilin da ya sa APC, Tinubu da shi kan sa su ka yanke shawarar amincewa Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Ya ce Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ne ya yi zurfin tunani da hangen nesa cewa kada Musulmi ya yi Shugaban Majalisar Dattawa.
Da ya ke wa Tajuddeen Abbas da tawagar sa bayani yayin da su ka kai masa ziyara a ranar Juma’a, Shettima ya ce sun fahimci bai kamata a ce Shugaba da Mataimaki da Kakakin Majalisa duk Musulmi ba ne, sannan kuma a ce Shugaban Majalisar Dattawa shi ma Musulmi ne ba.
Haka kuma ya ce Tinubu ba zai tafka irin kurakuren da Jonathan da Buhari su ka tafka ba.