Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta yi kakkausan gargaɗin cewa a wannan daminar akwai yiwuwar ɓarkewar mummunar ambaliya a Jihar Kwara.
Ofishin NEMA da ke Minna ne ya yi wannan gargaɗin, tare da sanar da mazauna yankunan cewa su yi shiri tun da wuri.
Hukumar ta shawarci mazauna ƙauyukan yankin, dagatai da shugabannin addinai cewa su su fara shiri tun da wuri, ta yadda za a rage irin ɓarnar da ruwan zai yi tun da wuri.
Gargaɗin dai na cikin wata sanarwa Shugaban Gudanar da Ayyukan Ceto na NEMA da ke Ofishin Minna ta bayar.
Zainab Suleiman-Sa’idu ce ta fitar da sanarwar a ranar Litinin. Ta ce gargaɗin ya zama tun da wuri, idan aka yi la’akari da sakamakon rahoton shekara-shekara da NIHSA ta fitar, sai kuma kirdadon da NiMET ta yi dangane da daminar 2023.
Ta ce masana kimiyya ne su ka yi binciken, tare da bayar da shawarar yiwuwar ambaliya sosai a faɗin ƙasar nan.
Ta ce rahoton na masana ya tabbatar da cewa ambaliya me da za a fuskanta jihar Kwara.
NEMA ta yi gargaɗin cewa mutanen da su ka san sun gina gidaje kan hanyar da ruwa ke bi, da waɗanda ke zaune gefen ruwa duk su tashi da daga inda su ke su koma kan tudu.
Discussion about this post