Hukumar NDLEA ta kama wasu ‘yan kasuwa biyu da suka hadiyi kullin hodar ibilis guda 193.
Shugaban hukumar Femi Babafemi a wata takarda da manema labarai suka samu ya bayyana cewa hukumar ta kama wadannan mutane a tashar jiragen saman Nnamdi Azikiwe a Abuja.
Babafemi ya ce mutanen su biyu sun yi bahayan hodar ibilis din bayan sun yi kwanaki uku tsare a hannun hukumar.
Ya ce hukumar ta kama Onoh Ebere mai shekara 49 da Christian Ifeanyi Ogbuji mai shekara 47 ranar 10 ga Mayu a jirgin saman Ethiopian airlines wacce ta taso daga kasar Uganda zuwa Najeriya.
Babafemi ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna wadannan mutane na da sana’o’in da suke yi amma safarar muggan kwayoyi na daga cikin hanyoyin da suke samun kuɗi.
“Wadannan mutane sun taso daga kasar Uganda sannan suka biya zuwa Addis Ababa domin karbo hodar ibilis din sannan suka shigo Najeriya da su har zuwa Abuja.
“Bayan kwanaki uku suna tsare a hannun NDLEA Ebere Onoh ya yi bahayan kullin hodar ibilis guda 100 sannan Christian Ifeanyi Ogbuji ya yi bahayan guda 93.
Babafemi ya ce hukumar ta kama kwalaben ruwan Akuskura 7,800 daga hannun wani Mohammed Kyari mai shekara 42 dake safarar maganin.
Ya ce hukumar ta kama Kyari ranar 10 ga Mayu a garin Gamboru Ngala dake karamar hukumar Jere a jihar Borno.
Discussion about this post